Kashim Ya Nada Dan Uwan Datti Baba-Ahmed A Matsayin Hadiminsa A Harkokin Siyasa

Kashim Ya Nada Dan Uwan Datti Baba-Ahmed A Matsayin Hadiminsa A Harkokin Siyasa

  • Kace-nace yayin da shugaban kasa, ya nada sabon mai ba Kashim Shettima shawara a kan harkokin siyasa
  • Tinubu ya nada kakakin Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, Dakta Hakeem Baba-Ahmed a matsayin mai ba shi shawara kan siyasa
  • Hakeem ya kasance dan uwa ga mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya na Hakeem Baba-Ahmed a matsayin hadimi bangaren siyasa ga mataimakinsa, Kashim Shettima.

Dakta Hakeem shi ne kakakin Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) kuma mai yawan sukar tsare-tsaren jam'iyyar APC mai mulki, Legit ta tattaro.

Tinubu ya nada Baba-Ahmed a matsayin hadimi a bangaren siyasa
Tinubu Ya Nada Dan Uwan Datti Baba-Ahmed A Matsayin Hadimi. Hoto: Bola Tinubu, Datti Baba-Ahmed, Hakeem Baba-Ahmed.
Asali: Facebook

Meye Tinubu ya nada Baba-Ahmed?

Hakeem ya kasance dan uwan Dakta Datti Baba-Ahmed, mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Shugaban APC Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Bayan Lakaɗa Wa Kwamishinar Mata Duka a Wurin Rabon Tallafi

Wannan mukamin ya bai jama'a mamaki ganin yadda Hakeem ya ke zazzagar jam'iyyar APC mai mulki.

Hakeem ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Litinin 18 ga watan Satumba.

Ya ce:

"Lokaci ya yi da zan sanar da duniya cewa na karbi mukamin mai ba da shawara a harkokin siyasa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
"Wannan ba lokaci ne na caccaka ba idan har ka samu damar sauya kasar ga tudun na tsira.
"Na yi matukar murna da wannan mukami, ku taya ni da addu'a da ma Nigeria baki daya."

Nadin Baba-Ahmed da Tinubu ya yi zai jawo cece-kuce?

Wannan mukami ya jawo cece-kuce yayin da mutane ke ganin yadda ya ke sukar jam'iyyar APC da tsare-tsarenta.

Dakta Hakeem ya kasance yaya ga Dakta Datti Baba-Ahmed, mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi da ke da bambancin siyasa da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Nada Muri-Okunola, Yakasai, Da Wasu 14 a Matsayin Hadimansa

Wannan shi ne karo na biyu da Bola Tinubu ke nada wani daga bangaren Datti Baba-Ahmed bayan nada Farfesa Tahir Mamman a matsayin ministan ilimi.

Tahir Mamman kafin nada shi mukamin, shi ne shugaban Jami'ar Baze da ke Abuja wanda Datti Baba-Ahmed ya mallaka.

Tinubu ya nada yaron El-Rufai mukami

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nada yaron El-Rufai, Muhammad Sani Dattijo a matsayin mataimakin gwamnan CBN.

Dattijo ya taba rike mukamin kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare a lokacin mulkin Nasir El-Rufai a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel