Mataimakin Gwamna Shuaibu Ya Fice Daga Gidan Gwamnati Tare Da Komawa Sabon Ofis

Mataimakin Gwamna Shuaibu Ya Fice Daga Gidan Gwamnati Tare Da Komawa Sabon Ofis

  • Philip Shuaibu ya fara kwashe kayansa daga ofishinsa da ke gidan gwamnati zuwa wani wuri na daban
  • Wannan na zuwa ne bayan mataimakin gwamnan ya janye karar da ya shigar a kotu kan uban gidan nasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu ya fara tattara kayansa daga gidan gwamnati zuwa wani sabon ofishi.

Shuaibu na shirin tattara kayansa ne zuwa wani da ke nesa da gidan gwamnatin jihar.

Shuaibu ya tattare kayansa daga ofishinsa na gidan gwamnti
Gwamna Obaseki da mataimakinsa, Shuaibu na Takun saka. Hoto: Godwin Obaseki.
Asali: Facebook

Meye ya jawo tarewar mataimakin gwamna, Shuaibu?

Wannan na zuwa ne bayan janye karar da Shuaibu ya yi a kotu na dakatar da Gwamna Obaseki daga cire shi a matsayinsa, Legit ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Cire tallafi: Shettima Zai rabawa talakawan jihohin Arewa 6 kayayyakin abinci

A baya Gwamna Godwin Obaseki da mataimakinsa sun sha samun matsaloli daban-daban wanda har ta kai ga gwamnan na kokarin tsige Shuaibu a mukaminsa.

Hakan ne ma ya sa Philip Shuaibu shigar da kara kotu inda ya ke rokon kotun ta dakatar da Obaseki daga tsige shi a mukamin.

Wata majiya tabbatarwa Channels TV cewa an tura wasika zuwa ga shugaban ma'aikata da ta tabbatar da tura takardu zuwa sabon ofishin mataimakin gwamnan.

Mataimakin gwamna, Shuaibu na takun saka da Obaseki

Wani faifan bidiyo da aka wallafa an gano sabon ofishin ba a kimtse ba kuma babu alamun an yi masa gyara.

Wata majiya ta bangaren mataimakin gwamnan ta ce babu wutar lantarki a ofishin bare sauran kayan more rayuwa.

Ta kara da cewa ruwa ya cika ofishin, sannan wurin ya yi karami a matsayin ofishin mataimakin gwamna.

Gwamnatin jihar ta tabbatar cewa ofishin na kusa da gidan gwamnatin jihar duk da cewa ba a ciki ya ke ba

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa

Shuaibu ya janye karar da ya shigar a kotu kan Gwamna Obaseki

A wani labarin, Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu, ya janye karar da ya maka gwamnan jihar, Godwin Obaseki, a gaban babbar kotun Tarayya.

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1027/2023, mataimakin gwamnan ya roki kotu ta dakatar da gwamna Obaseki daga yunkurin tsige shi daga kujerarsa.

Daga cikin wadanda sunayensu ke kunshe cikin karar akwai Sifetan 'yan sanda na kasa, Olukayode Egbetokun da hukumar tsaron farin kaya ta jiha (SSS) da gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel