Edo: Shaibu Ya Janye Karar da Ya Maka Gwamna Obaseki a Kotu Bayan Shiga Tsakani

Edo: Shaibu Ya Janye Karar da Ya Maka Gwamna Obaseki a Kotu Bayan Shiga Tsakani

  • Ga dukkan alamu an fara shawo kan rigimar da ta haɗa mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu da gwamna Obaseki
  • Mista Shaibu ya bayyana cewa ya janye ƙarar da ya shigar gaban babbar Kotun tarayya inda ya nemi a dakatar da gwamna Obaseki
  • Ya ce hakan ya biyo bayan shiga tsakanin da manyan masu faɗa aji suka yi kuma ba zai sa ƙafa ya take maganganun su ba

Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya janye ƙarar da ya maka gwamnan jihar, Godwin Obaseki, a gaban babbar Kotun tarayya, Channels tv ta ruwaito.

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1027/2023, mataimakin gwamnan ya roƙi Kotu ta dakatar da gwamna Obaseki daga yunƙurinsa na tsige shi daga kujerarsa.

Mataimakin gwamna, Philip Shaibu da gwamna Obaseki na Edo.
Edo: Shaibu Ya Janye Karar da Ya Maka Gwamna Obaseki a Kotu Bayan Shiga Tsakani Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Haka nan ƙarar na ƙunshe da sunayen sufetan 'yan sanda na ƙasa, hukumar tsaron farin kaya ta jiha (SSS), gwamnan Edo da Alkalin alƙalan jihar a matsayin waɗanda ake tuhuma.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 18 da Suka Lashe Zaɓe a Jiharsa

Meyasa mataimakin gwamnan ya janye ƙarar?

Mataimakin gwamna ya bayyana cewa ya ɗauki matakin janye karar ne bayan tarukan da suka gudanar, wanda ya haɗa shi kansa, gwamna Obaseki da wasu masu kishin Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, waɗanda suka halarci taron sasancin sun haɗa da shugabannin jam'iyyar PDP, Sarakuna da babban Malamin cocin Katolika.

A ruwayar Leadership, Shaibu ya ce:

“Tare da girmamawa ga wadannan fitattun mutane da shugabannin da ba zan iya watsi da rarrashinsu ba, ni, Kwamared Philip Shaibu na ba da izini kuma na umurci Lauyoyina da su janye karar nan take.”
“Ina so na mika godiya da jinjina ga wadannan ’yan Najeriya masu kishin kasa, shugabannin jam’iyya, Sarakunan Gargajiya, da Malami na, mai girma Rebaran Augustine Akubeze."
"Ina ƙara gode msusu bisa ga irin tausasan kalamai, nasiha da karfafa gwiwar da suka mun har ya zuwa yanzu wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a jihar Edo."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Naɗa Abokin Adawarsa Na NNPP Da Wasu Mutum 8 a Manyan Muƙamai

"Ina kuma so in mika godiyata ta musamman ga Mai girma Gwamna, maigidana da kuma babban ɗan uwana kan wannan hanya da ya bi don samun zaman lafiya."

Shugaban Ƙasar Guinea Bissau Ya Kara Wa Masu Tsaronsa Karfi

A wani rahoton na daban Shugaba Umaro Embalo na ƙasar Guinea-Bissau ya naɗa sabbin jami'ai a tawagar masu gadin shugaban ƙasa yayin da juyin mulki ke yaɗuwa a Afirka.

Embolo ya amince da naɗin Janar Tomas Djassi a matsayin shugaban dakarun tsaron shugaban ƙasa da kuma Janar Horta Inta a matsayin shugaban ma'aikatan shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel