Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa

Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa

  • An bukaci magoya bayan Peter Obi da Labour Party da Obidients da kada su yanke kauna duk da hukuncin kotun zaben shugaban kasa
  • Peter Obi ne ya umurce su da haka a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba, yana mai cewa yin hakuri ba zabi bane a wannan mawuyacin lokaci
  • Obi ya jinjinawa juriyar magoya bayansa da jajircewarsu wajen bijirewa masu mulkin mallaka da ba sa son sabuwar Najeriya

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben 25 ga watan Fabrairu ya bukaci magoya bayansa da kada su yanke kauna a yayin da kotun zaben shugaban kasa ta yanke hukunci.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na soshiyal midiya a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba, tsohon gwamnan na jihar Anambra, ya bayyana cewa basu cire rai ba kuma cewa yanzu suka fara fafutukar neman Najeriya mai inganci.

Kara karanta wannan

Yaro Dan Shekara 15 Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa Ya Nemi Gwamnan Arewa Ya Sa Hannu

Peter Obi ya yi jawabin farko bayan hukuncin kotun zabe
Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa Hoto: Mr Peter Obi/Kola Suliamon
Asali: UGC

Ya rubuta:

"A yau, ina so na isa gareku kai tsaye sannan na karfafa maku gwiwa da ku ci gaba da sa rai. Duba ga kalubalen da ke gabanmu a matsayin kungiya, yanke kauna ba zabi bane. Ba a samun abu mai kyau a rayuwa cikin sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A tarihi, sauye-sauye masu kyau suna zuwa ne kawai da sadaukarwa, hakuri, juriya da fadi tashi.
"Tun daga farkon tafiyarmu, na fada maku cewa tafiyar da muke kan farawa ba gajere bane, illa mai tsawo da wahala. Zai kasance mai wahala, radadi da tashin hankali."

Peter Obi ya jinjinawa yan Obidients

Obi ya bukaci yan Obidients da kada su mika wuya ga masu mulkin mallaka wadanda za su iya yin komai don hana canji mai kyau da gyara.

Ya ce ya samu karfin gwiwa da karfin yan Obidients na jure duk wasu wani abu da aka tunkarosu da shi.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yadda Al’umma Ke Cin Dusa Saboda Yunwa a Wata Jihar Arewa

Ya tabbatarwa magoya bayansa cewa sakamakon kotun zaben ya sake sa mai himma da jajircewa wajen gina sabuwar Najeriya.

Ya ce:

"Ina tabbatar muku da cewa za mu dage da himma har sai mun isa inda za mu je, dole ne Najeriya ta zama ta dukkan 'yan Najeriya ba na wasu zababbun mutane ba."

"Da yardar Allah sai na kammala wa’adin mulkina a raye", Gwamna Akeredolu

A wani labari na daban, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya koma bakin aiki a hukumance bayan hutun jinya na watanni uku da ya tafi a kasar Jamus.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba ne Akeredolu ya dawo gida Najeriya daga Jamus inda ya shafe watanni uku yana jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel