An Nemi Tinubu Ya Dakatar Da Wike, Umahi Da Sauran Tsoffin Gwamnoni Daga Karbar Fansho

An Nemi Tinubu Ya Dakatar Da Wike, Umahi Da Sauran Tsoffin Gwamnoni Daga Karbar Fansho

  • SERAP ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya hana ministocinsa, wadanda suka kasance tsoffin gwamnoni, karbar kudin fansho daga jihohinsu mabanbanta
  • Kungiyar ta yi gargadi kan yiwuwar daukar matakin shari'a idan ministocin suka ci gaba da karbar kudaden fansho yayin da suke aiki a gwamnati mai ci
  • Wadanda abun ya shafa sun hada da Nyesom Wike, Abubakar Badaru, Bello Matawalle, Gboyega Oyetola da sauransu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Da kuma tabbatar da adalci a hukumomi da Ma'aikatun gwamnati (SERAP), ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da ministocinsa, wadanda suka kasance tsoffin gwamnoni daga karbar kudin fansho daga jihohinsu.

Kungiyar mai zaman kanta ta yi kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Sojojin Da Suka Ji Rauni Da Kyautar Kudi Masu Yawan Gaske

SERAP na so a hana wasu ministoci cin fansho daga jihohinsu
An Nemi Tinubu Ya Dakatar Da Wike, Umahi Da Sauran Tsoffin Gwamnoni Daga Karbar Fansho Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, David Umahi, Nyesom Wike
Asali: Facebook

A cikin sanarwa da ta saki wanda Legit.ng ta gani, SERAP ta yi barazanar maka shugaban kasar na Najeriya a gaban kotu idan ya gaza dakatar da ministocin daga karbar fansho a matsayin tsoffin gwamnoni.

Jerin ministocin da abun yashafa

  • Nyesom Wike (jihar Rivers)
  • Abubakar Badaru (Jihar Jigawa)
  • Bello Matawalle (Jihar Zamfara)
  • Gboyega Oyetola (Jihar Osun)
  • David Umahi (jihar Ebonyi)
  • Simon Lalong (jihar Plateau)
  • Atiku Bagudu (jihar Kebbi)
  • Ibrahim Geidam (jihar Yobe)

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

"DA DUMI-DUMI: Mun bukaci shugaban kasa Tinubu da ya dakatar da tsoffin gwamnoni, Wike, Abubakar, Matawalle, Oyetola, Umahi, Lalong, Bagudu da Geidam daga karbar kudin fansho daga jihohinsu yayin da suke aiki a matsayin ministoci a gwamnatinsa, ko ya fuskanci mataki na shari'a."

Jama'a sun yi martani

Kara karanta wannan

Abubakar Momoh: Tsohon Malamin Sakandare, Tsohon Shugaban SUG, Da Wasu Abubuwa Kan Sabon Ministan Matasa

@rtsado01 ya yi martani:

"Matakin da ya dace."

@Great_Bobb ya ce:

"Idan ba don rashin doka ba, me zai sa su ci gaba da karbar fansho?"

@Pa_Pa_Jay ya ce:

"Kun fara kuma ko."

@Gokingvii

"Bata lokaci. Abun da kuke yi kawai shine shigar da kara. Ban taba ganin wani da ya fito da sakamako mai kyau ba."

An bayyana makudan kudaden da ministoci za su dunga karba na gida

A wani labarin kuma, mun ji cewa alawus din gidajen sabbin ministoci da aka nada na iya kaiwa naira miliyan 343.25 duk shekara.

Da wannan kudade da za a ware masu duk shekara, gwamnatin tarayya za ta kashe naira biliyan 1.37 kan wajen kwanan zababbun ministoci 45 cikin shekaru hudu.

Wannan alawus din ya kasance bisa bayanan da aka tattara daga wata takarda da aka samu a shafin yanar gizo na hukumar tattara kudaden shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel