Kungiyar SERAP ta sake shiga kotu da Shugaba Buhari, wannan karo a kan hana Twitter

Kungiyar SERAP ta sake shiga kotu da Shugaba Buhari, wannan karo a kan hana Twitter

  • Kungiyar SERAP ta na karar Gwamnatin Tarayya a wani kotu a Abuja
  • Lauyoyin kungiyar sun shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/496/2021
  • SERAP ta na so a hana hukuma haramtawa ‘Yan jarida aiki da Twitter

Kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project watau SERAP ta kai karar gwamnatin tarayya a gaban wani babban kotun tarayya a Abuja.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa kungiyar ta SERAP ta shigar da karar gwamnatin Najeriya ne a kan haramtawa ‘yan jarida amfani da shafin Twitter.

Matakin Gwamnati ya saba doka – SERAP

Kwanaki gwamnatin tarayya ta bakin hukumar NBC ta kasa, ta bada umarnin ka da wani gidan talabijin ko na rediyo ya yi aiki da Twitter wajen nemo rahotonsu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya hana amfani da Twitter a Najeriya

SERAP ba ta yarda da wannan umarni ba, wanda ta ce ya saba wa dokar kasa, don haka ta ke karar gwamnatin tarayya da Ministan yada labarai, Lai Mohammed.

A karar da kungiyar ta shigar, ta bukaci a taka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, NBC, da Lai Mohammed burki wajen sawa kafofin sada zumuntan zamanin ido.

Rokon kungiyar SERAP a kotu

Punch ta ce SERAP ta na so a hana gwamnati bibiyar abubuwan da gidajen jaridu suke yada wa.

Wannan kungiya mai kare hakkin jama’a ta na da’awar cewa gwamnatin Muhammadu Buhari, Ministan da hukumar NBC suna kokarin danne hakkin ‘yan Najeriya.

Lai Mohammed
Alhaji Lai Mohammed Hoto: www.bbc.com/pidgin
Asali: UGC

KU KARANTA: EFCC ta karbowa Gwamnati N45bn a madadin Hukumar NPA

“Kotu na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen kare dokar kasa, da tabbatar da cewa mutane sun tsaya a hurumin da tsarin mulki ya ba su iko.” Inji SERAP.

Rahotanni sun bayyana cewa Kolawole Oluwadare, Kehinde Oyewumi da Opeyemi Owolabi, su ne lauyoyin da su ka tsaya wa kungiyar SERAP a kotun tarayyar.

Lauyoyin sun roki Alkali ya hana gwamnati da hukumar NBC muzgunawa ko lafta tara a kan gidajen talabijin da rediyo saboda amfani da Twitter a wajen aiki.

Kwanakin baya kun ji cewa kamfanin Twitter ya bayyana damuwa a kan matakin gwamnatin Muhammadu Buhari na dakatar da ayyukanta kaf a kasar Najeriya.

Wata babbar manajar yada labarai ta Twitter na Turai, gabas ta tsakiya da Afrika, Sarah Hart, ta sanar da cewa kamfanin na duba lamarin domin a samu mafita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel