Tajudeen Abbas Ya Bayyana Sabbin Shugabannin Majalisar Wakilai Ta 10

Tajudeen Abbas Ya Bayyana Sabbin Shugabannin Majalisar Wakilai Ta 10

  • Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana sabbin shugabannin da zasu jagoranci majaliaa ta 10
  • Farfesa Julius Ihonvbere, mamban jam'iyyar APC mai mulki ne ya zama sabon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta ƙasa
  • Haka nan kuma Abbas ya karanta wasiƙa daga ɓangaren marasa rinjaye, wacce ta ƙunshi sabbin jagororin marasa rinjaje a majalisar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban majalisar wakilan tarayya, Honorabul Tajudeen Abbas, ya sanar da sunayen sabbin jagororin majalisar a zaman yau Talata, 4 ga watan Yuli, 2023.

Abbas ya ayyana Farfesa Julius Ihonvbere daga jihar Edo kuma mamban APC a matsayin sabon shugaban masu rinjaye da kuma Usman Kumo daga Gombe a matsayin mai ladabtarwa.

Zauren majalisar wakilan tarayya.
Tajudeen Abbas Ya Bayyana Sabbin Shugabannin Majalisar Wakilai Ta 10 Hoto: House of representatives
Asali: Facebook

Jagororin majalisar tarayya ta 10

Halims Abdullahi daga jihar Kogi ya zama sabon mataimakin shugaban masu rinjaye yayin da Oriyomu Onanuga ya samu nasarar zama mataimakin babban mai ladabtarwa.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Sanata Akpabio Ya Sanar da Sunayen Sabbin Jagororin Majalisar Dattawa Ta 10

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Cable ta rahoto Abbas na cewa baki ɗaya 'ya'yan APC a zauren majalisar sun aminta da sabbin shugabannin waɗan da suka fito daga jam'iyya mai mulkin ƙasa.

Kakakin majalisar ya yi wa jagororin addu'ar fatan alheri da nasara yayin da suka karɓi ragamar jagorancin majalisar tarayya ta 10.

NTA News ta kawo jerin sabbin jagororin majalisar wakilai kamar yadda Abbas ya karanto a zauren majalisa ranar Talata.

Ɓangaren masu rinjaye

Shugaban masu rinjaye - Julius Ihonvbere (APC, jihar Edo)

Mataimakin shugaban masu rinjaye - Abadullahi Ibrahim Halims (APC, jihar Kogi)

Babban mai ladabtarwa - Usman Bello Kumo (APC, Gombe)

Mataimakin babban mai ladabtarwa - Adewunmi Onanuga (APC, Ogun)

Bangaren marasa rinjaye

Shugaban marasa rinjaye - Kingsley Chinda (PDP)

Mataimakin shugaban marasa rinjaye - Aliyu Sani Madaki (NNPP)

Mai ladabtarwan marasa rinjaye - Ali Isa (PDP)

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

Mataimakin mai ladabtarwan marasa rinjaye - George Ebizimawo (Labour Party).

Majalisa Ta 10: Sanata Akpabio Ya Sanar da Sabbin Shugabannin Majalisar Dattawa

A wani labarin na daban kuma Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio,ya sanar da sunaƴen sabbin jagororin majalisa ta 10 ranar Talata, 4 ga watan Yuli.

Sanata Akpabio ya bayyana waɗanda suka samu nasarar zama shugaban masu rinjaye, marasa rinjaye, mai ladabtarwa da mataimakansu.

Sabbin jagororin majalisar sun haɗa da Sanata Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti a matsayin shugaban masu rinjaye da Sanata Dave Umahi daga Ebonyi a matsayin mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel