Tinubu Ya Dora Mun Alhakin Dawo Da Zaman Lafiya a Zamfara, Yerima

Tinubu Ya Dora Mun Alhakin Dawo Da Zaman Lafiya a Zamfara, Yerima

  • Sanata Sani Yerima ya ce shugaban ƙasa ya ɗora masa alhakin daidaita al'amuran jihar Zamfara da tabbatar da zaman lafiya
  • Tsohon Sanatan ya bayyana haka ne a Aso Villa jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Tinubu ranar Litinin, 3 ga watan Yuli
  • Ya ce ya ziyarci Bola Ahmed Tinubu ne domin taya shi murnar karban ragamar mulkin ƙasar nan

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sani Yerima, ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarce shi da ya tabbata an samu zaman lafiya da jituwa a Zamfara.

Sanata Yerima ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jaridan gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaban ƙasa a Villa ranar Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Sani Yerima.
Tinubu Ya Dora Mun Alhakin Dawo Da Zaman Lafiya a Zamfara, Yerima Hoto: dailytrust
Asali: Facebook

Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta yi wa katutu a shiyyar Arewa maso Yamma yayin da 'yan bindigan jeji da masu garkuwa suka hana mutane rawar gaban hantsi.

Kara karanta wannan

Yariman Bakura Ya Sanya Labule Da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Wata Alfarma 1 a Madadin 'Yan Bindiga

A fagen siyasa kuma, rigima ta yi ƙamari tsakanin gwamna Dauda Lawal da tsohon gwamnan da ya karɓa a hannunsa, Bello Matawalle.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Lawal na zargin Bello Matawalle da wawure dukiyoyin gidan gwamnati, lamarin da ta kai ga tura 'yan sanda har gida suka kwaso motoci 40.

Wane mataki Yerima ke shirin ɗauka a Zamfara?

Yerima ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa domin tabbatar da cewa duk waɗan nan rigingimun sun zama tarihi a jihar Zamfara.

"Kamar yadda kuke faɗa ni Uba ne a Zamfara, shi kansa shugaban kasa, da muka keɓe da yammacin nan, ya nemi na yi duk mai yuwuwa wajen daidaita al'amura a jihar kuma dama aikin da muke yi kenan."
"Idan Allah ya so zaku ganmu tare mun haɗa kai wuri guda kuma zaku ga duk waɗan nan rigingimun sun zama tarihi."

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Matsaya Kan Cire Tallafin Mai da Wasu Tsarukan Shugaba Tinubu

- Sani Yerima.

Meyasa ya kai wa shugaban ƙasa ziyara?

Game da maƙasudin zuwansa fadar shugaban kasa, Yerima ya kara da cewa ya je wannan ziyara ne domin taya shugaba Tinubu murnar kama aiki kuma ya fara da kafar dama.

Ya ce daga hawan shugaban ƙasa ya ɗauki matakai uku, waɗanda ya yi imanin za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Bazata, Ya Kama Jami'an Lafiya Na Aikata Laifi

A wani rahoton na daban kuma Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kai ziyarar ba zata babban Asibitin Dutse ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023.

Yayin wannan ziyara, gwamna Namadi ya kama ma'aikatan lafiya suna siyar da magungunan da ake rabawa kananan yara kyauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel