Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

  • Da alama APC ta gamsu Michael Opeyemi Bamidele ya zama shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa
  • Sanata Muhammad Ali Ndume zai zama mai tsawatarwa, mataimakinsa zai fito ne daga Kudancin Kwara
  • Julius Ihonvbere, Dauda Kumo da Adewunmi Onanuga za su iya samun mukamai a majalisar wakilai ta kasa

Abuja - Watakila jam’iyyar APC mai rinjaye ta shawo kan sabanin da ake da shi a majalisar tarayya, ta yi rabon duk wadanda za a ba shugabanci.

Jam’iyya mai-mulki ta tafi da duk wasu manyan Sanatocin da ke neman mukamai ta yadda ba za a samu rikici ba, The Nation ta fitar da wannan labari.

Bayan an kai-an komo, APC tayi zama da shugabanninta a bangarori dabam-dabam, a karshe aka cin ma matsaya a kan wadanda za su samu kujeru.

Majalisar Dattawa
Sanatoci a Majalisar Dattawa Hoto: @NgrSenate
Asali: Twitter

Rahotonni sun nuna yau ko gobe jam’iyya ta rubuta takarda zuwa Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas domin sanar da su matsayar da ta dauka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta ce an tsaida maganar kujerar shugaban masu rinjaye da masu tsawatarwa.

Wadanda za a ba mukamai a Majalisa

Opeyemi Bamidele da Ali Ndume sun bada gudumuwa ga nasarar Godswill Akpabio/Barau Jibrin, saboda haka APC ta ke so dukkansu su samu matsayi.

Yadda aka yi rabon kuwa shi ne, Sanatan Ekiti Michael Opeyemi Bamidele daga Kudu maso yamma zai zama sabon shugaban masu rinjaye a majalisar.

Mataimakin shugaban masu rinjayen zai zama Dave Umahi mai wakiltar Kudancin Ebonyi.

Sanatan Borno ta Kudu, Muhammad Ali Ndume zai samu kujerar mai tsawatarwa, wanda zai zama mataimakinsa shi ne Sanata Lola Ashiru daga Jihar Kwara.

Majiyar take cewa su na fata sauran Sanatoci za su amince da wannan rabo da aka yi, jam’iyyar APC mai-ci ta na sa ran a haka ne za a samu zaman lafiya.

Majalisar Wakilan Tarayya

A majalisar wakilan tarayya, ana tunanin Farfesa Julius Ihonvbere zai zama shugaban masu rinjaye. Hon. Ihonvbere ya na wakiltar Owan a Edo.

Dauda Kumo daga Akko zai zama mai tsawatarwa, sai ‘yar majalisar Ikenne/Sagamu/Remo, Hon. Adewunmi Onanuga za ta uta zama mataimakiyarsa.

Rahoton ya ce Patrick Abba Moro ya na son zama shugaban marasa rinjaye. Watakila zai gwabza da Aminu Tambuwal, Adamu Aleiro da Abdul Ningi.

Akwai yiwuwar Sanata Irete Kolo Kingibe ta samu kujera a bangaren marasa rinjaye.

A makon yau za a gwabza

A baya rahoto ya yi bayanin cewa za a san wadanda za su zama shugabannin masu rinjaye, marasa rinjaye da masu tsawatarwa a majalisun Najeriya.

Za a goge raini tsakanin Michael Opeyemi Bamidele Bamidele Ali Ndume a APC. Kawunan ‘yan adawa ya rabu tsakanin Aminu Tambuwal da wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel