A Karon Farko a Tarihin Jihar Ebonyi, Gwamna Ya Nada Mace a Matsayin SSG

A Karon Farko a Tarihin Jihar Ebonyi, Gwamna Ya Nada Mace a Matsayin SSG

  • Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya naɗa mace a matsayin Sakatariyar gwamnatin jiha (SSG) karo na farko a tarihi
  • Rahoto ya nuna cewa gabanin naɗa ta SSG, Farfesa Grace Umezurike, lakcara ce a jami'ar jihar Ebonyi da ke Abakaliki
  • Ita ce mace ta farko da ta zama SSG a tarihin jihar Ebonyi kuma sanarwan ta ce naɗin zai fara aiki ne nan take

Ebonyi State - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya naɗa Farfesa Grace Umezurike a matsayin Sakatariyar gwamnatin jiha (Secretary to the State Government, SSG).

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wannan naɗin da gwamna Nwifuru na jam'iyyar APC ya yi, ya sa ta zama mace ta farko da ta zama SSG a tarihin jihar Ebonyi.

Farfesa Grace Umezurike.
A Karon Farko a Tarihin Jihar Ebonyi, Gwamna Ya Nada Mace a Matsayin SSG Hoto: punchng
Asali: UGC

Wannan naɗi na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na mai girma gwamna, Dakta Monday Uzor, ya rattaba wa hannu kuma ya fitar a Abakaliki.

Kara karanta wannan

Zaben 2024: Ɗan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka Daga Jam'iyyar PDP Zuwa LP

Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan naɗin na zuwa ne awanni kaɗan bayan gwamna Nwifuru, ya rantsar da manyan mataimaka na musamman guda 2 da kuma kananan mataimaka na musamman 20 ranar Jumu'a, 9 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwan, naɗin Farfesa Grace Umezurike a matsayin sabuwar Sakatariyar gwamnatin jiha zai fara aiki nan take.

Sanarwan ta ce:

"Gwamnan jihar Ebonyi, mai girma Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru, ya amince da naɗin Farfesa Grace Umezurike a matsayin Sakatariyar gwamnatin jiha.
"Wannan mataki zai fara aiki ne nan take. Za'a rantsar da ita ta kama aiki daga ranar Talata, 13 ga watan Yuni. 2023."

Wacece sabuwar SSG a jihar Ebonyi?

Gabanin naɗa ta SSG, Farfesa Grace Umezurike tana aikin koyarwa a jami'ar jihar Ebonyi da ke Abakaliki, babban birnin jihar da ke Kudu maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Haka nan kuma bayanai sun tabbatar da cewa sabuwar SSG mata ce ga tsohon kwamishinan lafiya da ya gabata a jihar, Dakta Daniel Umezurike.

Gwamna Fubara Ya Gana da Yan Majalisun Tarayya na jihar Ribas

A wani labarin na daban kuma Gwamna Fubara ya bayyana waɗanda mambobin majalisar tarayya na Ribas zasu zaɓa a matsayin shugabannin majalisa ta 10.

Idan zaku iya tunawa, Gwamnatin Jihar Ribas ta yi alƙawarin goyon bayan duk waɗanda jam'iyyar APC da shugaban kasa suka nuna suna so a majalisar tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel