Gwamna Fubara Ya Gana da Yan Majalisun Tarayya, Ya Fada Musu Wanda Zasu Zaba a Majalisa Ta 10

Gwamna Fubara Ya Gana da Yan Majalisun Tarayya, Ya Fada Musu Wanda Zasu Zaba a Majalisa Ta 10

  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya gana da Sanatoci da yan majalisar wakilan tarayya na jihar a gidan gwamnatinsa da ke Patakwal
  • Ya umarci Sanatoci su zabi Sanata Akpabi, su kuma yan majalisar wakilai su zaɓi Abbas a matsayin shugabannin majalisa ta 10
  • Jihar Ribas ta yi alƙawarin goyon bayan duk waɗan jam'iyyar APC da shugaban kasa suka nuna suna so a majalisar tarayya

Rivers - Gwamnan jihar Ribas wanda ya gaji Wike, Siminalayi Fubara, ya umarci Sanatocin jihar su zaɓi Sanata Godswill Akpabio, a matsayin shugaban majalisar Dattawa ta 10.

A wata sanarwa, gwamnan ya kuma umarci mambobin majalisar wakilai na jihar Ribas su zaɓi Tajudeen Abbas a matsayin kakakin majalisa wakilan tarayya ta 10.

Siminalayi Fubara.
Gwamna Fubara Ya Gana da Yan Majalisun Tarayya, Ya Fada Musu Wanda Zasu Zaba a Majalisa Ta 10 Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamna Fubara ya basu wannan umarnin ne yayin ganawa da zababbun 'yan majalisar tarayya na jihar Ribas wanda ya gudana a gidan gwamnatinsa da ke Patakwal.

Ya ce jiharsa zata goyi bayan Sanata Akpabio da Honorabul Abbas a matsayin shugabannin majalisa ta 10 ba don komai ba sai don, "Kishin ƙasa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun mai girma gwamna, Boniface Onyedi, ya wallafa a shafinsa na dandalin Facebook.

Sanarwan ta ce:

"Gwamnan jihar Ribas ya buƙaci zababbun yan majalisun tarayya da su tsaya kan kishin jiharsu kama su maida hankali wajen zaben waɗanda aka tsayar su shugabanci majalisa ta 10."
"Ya kuma shawarci zababbun yan majalisun, a ko da yaushe su riƙa aiki tare a matsayin tsintsiya ɗaya domin ta haka ne kawai zasu yi tasiri kuma su amfana da abinda zai biyo baya."

Idan baku manta ba, Akpabio da Abbas, su ne 'yan takarar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da jam'iyyar APC su ke goyon baya a matsayin shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai.

Nyesom Wike, ya tabbatarwa Akpabio cewa mambobin majalisar tarayya daga jihar Ribas zasu goyi bayan duk 'yan takarar da jam'iyyar APC ta tsayar saboda, "Amfanin ƙasa."

Da yake martani a madadin 'yan majalisun, Zababben Sanatan Ribas ta kudu maso gabas, Barry Mpigi, ya gode wa gwamna Fubara bisa haɗa taron kana ya tabbatar masa zasu cika umarnin da ya basu.

Mun Kwato Motoci Masu Tsada 40 a Gidan Matawalle, Gwamnatin Zamfara

A wani labarin na daban kuma Gwamnatin Zamfara ta yi karin haske kan samamen da yan sanda suka kai gidan Bello Matawalle.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Suleiman Idris, ya fitar, ya ce sun kwato motoci 40 yayin samamen ranar Jumu'a 9 ga watan Yuni, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel