Masu Ba Da Shawara Na Musamman Da Wasu Nade-Nade Da Tinubu Zai Iya Yi Ba Tare Da Neman Yardar Majalisa Ba

Masu Ba Da Shawara Na Musamman Da Wasu Nade-Nade Da Tinubu Zai Iya Yi Ba Tare Da Neman Yardar Majalisa Ba

  • Yan Najeriya sun matsu su ga wadanda sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai nada a majalisarsa don taimaka masa wajen gudanar da harkokin kasar
  • Zuwa yanzu, Shugaba Tinubu ya ambaci sunayen wasu yan majalisarsa, wadanda suka hada da Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikata da George Akume a matsayin SGF
  • Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da mambobin majalisarsa cikin kwanaki 60 bayan kama mulki

Abuja - Yan Najeriya sun kosa da son ganin jerin sunayen mambobin majalisar shugaban kasa Bola Tinubu.

Mambobin majalisar za su yi aiki tare da shugaban kasar don kula da harkokin kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Shugaban kasa Tinubu da wasu yan siyasa
Masu Ba Da Shawara Na Musamman Da Wasu Nade-Nade Da Tinubu Zai Iya Yi Ba Tare Da Neman Yardar Majalisa Ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz
Asali: Facebook

Zuwa yanzu, Shugaban kasa Tinubu ya sanar da tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata George Akume, a matsayin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).

Ya kuma nada kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a matsayin shugaban ma'aikatan shugaban kasa, da kuma Sanata Ibrahim Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sansanin shugaban kasar ya yi alkawarin cewa zai yi cikakken nade-nadensa cikin kwanaki 60 bayan rantsar da shi, jaridar The Guardian ta rahoto.

Wannan ya yi daidai da wani kudiri da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar wanda ya wajabtawa shugaban kasa da gwamnoni gabatar da sunayen mutanen da suka zaba a matsayin ministoci ko kwamishinoni cikin kwanaki 60 da karbar ransuwar aiki don majalisar dattawa ko majalisar dokokin jihar ta tabbatar da su, Daily Trust ta rahoto.

Koda dai majalisar dokoki ce za ta tabbatar da wasu nade-naden Tinubu, wasu basa bukatar amincewarsu.

Ga wasu daga cikinsu a kasa:

1. Bai ba kasa shawara kan harkokin tsaro

Ofishin mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ya kunshi bangarori daban daban da suka hada da rundunar soji, bangaren doka, hukumomin leken asiri, hukumomin kasa da kasa, kula da harkokin kudi, da sauransu.

Ana hasashen tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Nuhu Ribadu ne za a baiwa wannan kujerar.

2. Mai ba shugaban shawara na musamman kan kafofin watsa labarai

Mukamin mai ba shugaban kasa shawara na musamman matsayi ne na tallafawa a bangaren zartarwa na Najeriya, wanda aikinsa shine taimakawa shugaban kasar Najeriya wajen aiwatar da ayyukansa.

Wannan mukami shine na kakakin shugaban kasa a hukumance.

Mutum na karshe da ya hau wannan matsayi shine Femi Adesina.

3. Babban mai bayar da shawara kan harkokin labarai

Duk wanda ya hau kan wannan matsayi zai taka muhimmiyar rawar gani wajen inganta bangaren yada labarai.

Garba Shehu, tsohon shugaban kungiyar marubutan Najeriya wato NGE, shine ya rike mukamin na tsawon shekaru 8.

Ana hasashen masu biyayya ga Tinubu kamar sun Bayo Onanuga da Tunde Rahman da tsohon mataimakin babban editan Daily Trust, Abdulaziz Abdulaziz, sune ke hararar mukamin.

Tuni aka fara ganin Abdulaziz a kusa da shugaban kasar tun bayan rantsar da shi a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

"Ba zan ba ku kunya ba a matsayin SGF": Gorge Akume ya daukarwa yan Najeriya alkawari

A wani labarin, mun ji cewa sabon sakataren gwamnatin tarayya da aka rantsar, George Akume, ya daukarwa yan Najeriya alkawari bayan Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shi a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni.

Akume ya yi alkawari cewa ba zai ba yan Najeriya, Shugaban kasa Tinubu da jam'iyyarsa ta All Progressive Congress (APC) kunya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel