Tinubu Ya Sanar Da Nadin Gbajabiamila A Hukumance, Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa Ya Samu Mukami Shima

Tinubu Ya Sanar Da Nadin Gbajabiamila A Hukumance, Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa Ya Samu Mukami Shima

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Kakakin Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya a matsayin shugaban fadar ma'aikatansa
  • Shugaban ya yi nadin ne a hukumance yayin ganawar da ya yi da mambobin kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC a gidan gwamnati da ke Abuja
  • Gbajabiamila, wanda ya kasance mamba na majalisar wakilai na Najeriya tun 2003, za koma fadar shugaban kasa inda zai yi aiki a matsayin shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasar

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sanar da nadin Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya a matsayin Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa.

Shugaban kasar kuma ya amince da nadin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, a matsayin Mataimakin Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, TVC ta rahoto.

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Tolu Ogunlesi shima ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya wallafa hoton takardar nadin.

A cewar sanarwar da Legit.ng ta gani mai dauke da sa hannun Abiodun Oladunjoye, daraktan watsa labarai, shugaban kasar ya sanar da hakan ne yayun ganawarsa da mambobin kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC a ranar Juma'a 2 ga watan Yuni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Takaitaccen tarihin siyasar Gbajabiamila

An fara zaben Gbajabiamila ne a Majalisar Wakilai na Tarayya don wakiltar Surulere 1 a Legas a 2003. Daga bisani ya zama Kakakin Majalisa.

Gbajabiamila ya zama Kakakin Majalisa ne bayan lashe tazarcensa na karo na biyar a majalisar.

An sake zaben kakakin karo na shida amma bisa alamu zai ajiye mukamin a yanzu.

An rahoto cewa ya bar takardan shaidansa na cin zabe a hannun Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, bayan cin zaben majalisar na 2023.

Kafin nadinsa, an rika samun jita-jita cewa Gbajabiamila ne aka nada shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Manyan yan siyasa a kasar ciki har da Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, tunda farko ya taya Gbajabiamila murnar samun sabon mukaminsa.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel