“Ba Zan Ba Da Kunya Ba”: Gorge Akume Ya Daukarwa Yan Najeriya Alkawara a Matsayin Sabon SGF

“Ba Zan Ba Da Kunya Ba”: Gorge Akume Ya Daukarwa Yan Najeriya Alkawara a Matsayin Sabon SGF

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon babban sakataren gwamnatin tarayya
  • Sabon SGF da aka rantsar ya sha alwashi cewa ba zai bai wa yan Najeriya, Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa ta APC kunya ba
  • Akume wanda aka nada a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni, ya kuma yi alkawarin bin sahun Shugaban kasa Tinubu

Abuja - Sabon sakataren gwamnatin tarayya da aka rantsar, George Akume, ya daukarwa yan Najeriya alkawari bayan Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shi a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Akume ya yi alkawari cewa ba zai ba yan Najeriya, Shugaban kasa Tinubu da jam'iyyarsa ta All Progressive Congress (APC) kunya ba.

Sabon sakataren gwamnatin tarayya, George Akume
“Ba Zan Ba Da Kunya Ba”: Gorge Akume Ya Daukarwa Yan Najeriya Alkawara a Matsayin Sabon SGF Hoto: Senator Dr George Akume
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na jihar Benue ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan shugaban kasa Tinubu ya rantsar da shi a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Lissafa Jerin Mukamai 5 Da Bai Kamata Shugaban Kasa Tinubu Ya Ba Yan Siyasa Ba

Akume ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Zabana da aka yi cikin yan Najeriya fiye da miliyan 200 don yin aiki a wannan matsayin, kalubale na yin aiki daidai da rantsuwar da na dauka a yau.
"Ina mai ba yan Najeriya tabbaci zan yi iya bakin kokarina, ba zan ba shugaban kasa kunya ba, ba zan ba kasar nan kunya ba kuma ba zan ba jam'iyyata kunya ba.
"Na yarda yan Najeriya za su samu cikar buri a ayyukana yayin da nake sauke su daidai da muradinsu. Babban karramawa yi wa kasar nan hidima kuma ina da yakinin cewa tare da jagorancin Allah madaukakin sarki, zan yi iya bakin kokarina kuma yan Najeriya za su kurbi ruwan damokradiyya."

Akume ya yi alkawarin bin sahun Shugaban kasa Tinubu

Akume, wanda ya kasance minista karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gabata, ya ce zai bi sahun Shugaban kasa Tinubu domin ba zai so ya ba da kunya ba, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Da Gaske Dan Shugaban INEC Ya “Haukace” a Saudiyya? Gaskiya Ta Bayyana

"Ni mutum ne da ya kasance a tsarin na tsawon lokaci kuma na san mutumin da muke yi wa aiki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa kuma ya zama dole mu bi sahunsa.
"Bai taba kasancewa a wajen kallo ba, wanda ke cike da suka ba. A kodayaushe yana cikin bagire, inda masu yi suke. Shi mai yi ne, don haka ya zama dole mu shiga ayi da mu. Dole ba za mu yarda mu gaza ba."

Gambari ya mika mulki ga Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'akatan shugaban kasa

A wani labarin, mun ji cewa Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikatan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika mulki ga magajinsa, Femi Gbajabiamila.

Bikin mika mulkin wanda ya samu halartan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gudana ne a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel