Shugaban Ma’aikatan Tinubu: Daga Karshe Gbajabiamila Ya Magantu

Shugaban Ma’aikatan Tinubu: Daga Karshe Gbajabiamila Ya Magantu

  • Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya magantu kan rade-radin da ake yi cewa an nada shi shugaban ma'aikatan shugaban kasa Bola Tinubu
  • Gbajabiamila ya bukaci jama'a da su yi hakuri sannan su bari tsari ya yi aikinsa kan wannan kujera
  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya ce idan har hakan ya kasance toh lallai Tinubu ya yi tunani mai kyau

Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi martani ga rahotannin cewa an nada shi a matsayin shugaban ma'aikatan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Ana ta alakanta Gbajabiamila da wannan kujera tun bayan da Tinubu ya bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Shugaban kasa Bola Tinubu da Femi Gbajabiamila
Shugaban Ma’aikatan Tinubu: Daga Karshe Gbajabiamila Ya Magantu
Asali: Facebook

A safiyar yau Alhamis ne rahotanni suka bayyana cewa shugaban kasar ya zabi Gbajabiamila bayan shafe tsawon awanni da dama ana taruka da tattaunawa.

Kara karanta wannan

Da Gaske An Nada Femi Gbajabiamila Shugaban Ma’aikatan Tinubu? Femi Fani-Kayode Ya Magantu

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Tinubu tare da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, a ranar Alhamis, Gbajabiamila ya ce mutane su bari tsarin ya yi aikinsa, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ku yi hakuri, ku yi hakuri, tsarin na da ka'idarsa na aiki. Mu bari tsarin ya yi aiki," cewarsa yayin da yake amsa tambaya kan dalilin da yasa ba a sanar da nadin nasa ba a hukumance yayin da sakonnin taya murna ke ta shigo masa.

Da aka tambaye shi ko za a sanar kafin karewar yau, sai ya ce:

"Za mu gani, za mu gani, za mu gani. Nagode sosai."

Lawan ya yi martani kan nadin Gbajabiamila

A nashi bangaren, Lawan ya ce yana jiran jin sanarwa a hukumace, yana mai cewa, "Idan haka ta kasance, shugaban kasa ya yanke shawara mai cike da hikima.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakaki, Bayanai Sun Fito

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

"Da farko, ina rokon Allah yasa hakan ya faru. Idan ya faru, mai girma shugaban kasa ya yanke shawara mai kyau. A halin yanzu, kana bukatar shugaban ma'aikata mai tarin gogewa a bangaren dokoki, ta bangaren hada kai da bangaren zartawa wanda kakakin majalisar ya yi jagoranci a majalisar.
"Yana da kyakkyawar alaka da goyon bayan da ake bukata. kuma idan hakan ya faru, kun san cewa wamman gwamnati za ta zama gwamnatin yan majalisar tarayya.
"Kuna da shugaban kasa wanda ya taba yin sanata, mataimakin shugaban kasa wanda ya kasance sanata da kuma shakka babu wanda zai iya zama shugaban ma'aikatanmu, kakakin majalisar wakilai, mutum ne wanda yake majalisar dokoki tsawon shekaru 20."

A wani labarin kuma, mun ji cewa jigon APC, Femi Fani-Kayode ya taya Gbajabiamila murnar zargin nada shi shugaban ma';aikatan Tinubu.

A cewar Fani-Kayode, kakakin majalisar wakilan ya cancanci hawa wannan kujera mai daraja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel