Naɗin Muƙamai: Kiristocin Najeriya Sun Fadawa Tinubu Abin da Suke So a Mulkinsa

Naɗin Muƙamai: Kiristocin Najeriya Sun Fadawa Tinubu Abin da Suke So a Mulkinsa

  • Kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN ta aika wani sako na musamman zuwa ga Bola Ahmed Tinubu
  • Shugaban CAN ya fitar da jawabi inda ya roki sabon shugaban kasan ya zama mai adalci da gaskiya
  • Daniel Okoh ya na so gwamnatin Tinubu ta gyara kura-kuran da ya ce shugabanni sun rika yi a baya

Abuja - Kungiyar kiristocin Najeriya watau CAN tayi kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da adalci wajen nadin mukamai.

Tribune ta kawo rahoto cewa kungiyar ta CAN ta na so Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya tafi da kowa idan zai nada hafsun sojojin Najeriya.

Haka zalika a duk sauran manyan mukaman siyasa da za a raba, kiristocin kasar su na so a dama da kowa domin gwamnati ta ji dadin aikinta.

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Bola Tinubu ya rantsar da SGF
Bola Tinubu ya rantsar da SGF Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Sanarwar ta fito ne a wani jawabi da ya fito daga ofishin shugaban kungiyar CAN na kasa, Archbishop Daniel Okoh a yammacin ranar Talatar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daniel Okoh ya ce yana da muhimmanci a samu wakilcin kwararrun da su ka san aiki daga kowace kabila da addini idan an tashi yin rabon kujeru.

Vanguard ta ce Okoh ya na zargin cewa an yi rashin daidai a baya a wajen nadin mukamai, ya na mai fatan wannan karo abubuwa su sake zani.

Jawabin Shugaban CAN

"Kungiyar CAN ta fahimci muhimmancin wadannan mukamai wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin ‘yan kasa.
Saboda haka mu na ba Shugaban kasa Tinubu shawara tun wuri ya dauki matakin tabbatar da adalci wajen nadin mukamai.
A tafi da kowa, kuma a tabbata an zakulo wadanda suka fi dacewa domin rike mukaman.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aikin Gama Gari, Ta Ba Gwamnatin Tinubu Sabon Wa’adi

Mutanen Najeriya su na zura ido domin ganin an samu gwamnatin da za ta shawo kan rashin adalci da zaluncin da aka rika yi a baya.
Sannan mu na fata Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi amfani da wannan damar mukaman nan domin cire dar-dar din ‘yan kasa.

- Daniel Okoh

Matsayar Abdulaziz Yari

An samu labari cewa Abdulaziz Yari ya ce Ubangiji kadai zai yi hukunci kan wanda zai zama Shugaban Majalisa, ya gargadi masu neman yin shisshigi.

Yari yake cewa Allah (SWT) da ake bauta ne kadai ya ke da ikon bada mulki, ba wani ‘Dan Adam ba, da alama ya na raddi ne ga masu rike da madafan iko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel