Cire Tallafin Man Fetur: NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Na Gama Gari a Ranar Laraba

Cire Tallafin Man Fetur: NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Na Gama Gari a Ranar Laraba

  • Shugabancin kungiyar kwadago ta sanar da shirin shiga yajin aikin gama hari daga ranar Laraba mai zuwa
  • Hakan na daga cikin shawarar da suka yanke a wani taron shugabannin kungiyar na kasa da ya gudana a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni
  • Sun yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan Shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana cewa zamanin tallafin man fetur ya tafi har abada a jawabin rantsar da shi

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta tabbatar da shirinta na shiga yajin aikin gama gari wanda zai fara daga ranar Laraba mai zuwa, jaridar Punch ta rahoto.

Wannan ci gaban na zuwa ne a lokacin da ake tsaka da fama da karancin man fetur a fadin kasar sakamakon jawabin rantsarwa na Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda a ciki ya ayyana cewa an cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Shugaban kasa Bola Tinubu da Joe Ajaero
Cire Tallafin Man Fetur: NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Na Gama Gari a Ranar Laraba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Cire tallafin mai: NLC ta yi barazana ga FG

Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ne ya bayar da sanarwar bayan wani taron gaggawa da kwamitin NEC na kungiyar ya gudanar a Abuja a ranar Juma'a, 2 ga watan Yunin 2023, Channels TV ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce gwamnatin, musamman kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) tana da daga yanzu zuwa ranar Laraba mai zuwa ta koma siyar da man fetur a kan tsohuwar farashi.

Ajaero ya kara da cewar idan har gwamnati ta ki ba da hadin kai har wa'adin ya cika toh za su yi zanga-zangar har sai baba ta gani a fadin kasar.

Dan majalisar Adamawa ya koma hawa keke saboda tsadar man fetur

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban masu tsawatarwa a majalisar dokokin jihar Adamawa, Hon. Haruna Jilantikiri, ya ce ya komawa hawan keke domin yin zanga-zanga ga tashin farashin man fetur.

Kara karanta wannan

Manajan NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

Dan majalisar, wanda ke wakiltan mazabar Madagali a majalisar jihar, ya ce ya yanke shawarar ajiye motarsa da amfani keke don gudanar da harkokinsa na yau da kullun.

An samu kari a farashin man fetur inda ya ninka ya kai sau uku bayan sabon shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewar daga yanzu zamanin tallafin man fetur ya wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel