An Gagara Shawo Kan Tsohon Gwamnan APC, Ya Dage da Neman Shugabancin Majalisa

An Gagara Shawo Kan Tsohon Gwamnan APC, Ya Dage da Neman Shugabancin Majalisa

  • Abdulaziz Yari ya ki jin lallashin APC, ya ce Ubangiji kadai zai zabi Shugaban Majalisar Tarayya
  • Zababben Sanatan Jihar Zamfara ta yamma ya aika sako ga wadanda suke ganin mulki ya na hannunsu
  • Yari ya yi wannan bayani ne a lokacin da ‘Yan Kudu maso kudu mazauna garin Abuja su ka ziyarce shi

Abuja - Zababben Sanata da zai wakilci Zamfara ta yamma a majalisar dattawa, Abdulaziz Yari, bai da niyyar hakura da takarar da yake yi a karkashin APC.

The Cable ta rahoto Abdulaziz Yari ya na mai cewa Ubangiji Madaukakin Sarki ne kurum zai zabi wanda zai jagoranci majalisar dattawa ba wani ‘Dan Adam ba.

Jam’iyyar APC mai-ci ta zabi tsohon Ministan harkokin Neja-Delta, Sanata Godswill Akpabio a matsayin ‘dan takaranta, amma sam Abdulaziz Yari bai sallama ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Taimaki APC Wajen Raba Kan ‘Yan Adawa a Zaben Majalisa

Shugabancin Majalisa
Abdulaziz Yari a wani taro Hoto: Hon Kamilu Saidu Wambai (Wamban Kasuwardaji)
Asali: Facebook

Da yake magana da kungiyar mutanen Kudu maso kudu da suka kai masa ziyara, zababben Sanatan ya ce a karshe kaddarar Ubangiji (SWT) za tayi aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An rahoto tsohon Gwamnan na jihar Zamfara ya nuna babu dalilin yin rigima a kan shugabancin majalisar tarayyar, yake cewa a bar wa Ubangiji ikonsa.

Jawabin Abdulaziz Yari

“Mutane su guji fada da Ubangiji, Ubangiji ne kurum, Allah (SWT) da mu ke bauta ne kadai ya ke da ikon bada mulki, ba wani mutum ba.
Ubangiji ne yake daura mutum a mulki ya zabi wanda zai zama shugaba. Wannan kira ne ga duk mai tunanin zai iya bada mulki ko ya karbe.
Wadanda suke kan karagar mulki su tuna cewa Ubangiji ne ya ba su mulki kuma Ubangijin nan bai taba motsawa daga inda yake.

Kara karanta wannan

Zababben Sanata Zai Birkita APC, Ya Jawo Tinubu Ya Zauna da Shugabannin Majalisa

Wannan kira ne ga babbar murya ga kowa. Ubangiji ne kawai, abin da Allah ya zartar ne zai faru.

- Abdulaziz Yari

Za ayi aikin Ogoni a Neja Delta

Yari ya shaidawa wadanda suka ziyarce shi cewa muddin ya samu wannan kujera, gwamnati za tayi kokarin ganin an kammala aikin gyaran Ogoni.

Mike Okiro wanda shi ne jagoran wannan kungiya ta mutanen Kudu maso kudu da ke zama a Abuja, ya nunawa Yari cewa su na tare da shi a takarar.

Bola Tinubu ya kira taro

An ji labari Bola Tinubu zai yi bakin kokarinsa na ganin mutanensa sun rike majalisa, zai hadu da Sanatoci domin ganin nasarar Godswill Akpabio.

Sabon shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya roki Yusuf Gagdi, Sada Soli, Muktar Betara, da sauran 'Yan G7 su bi bayan Tajuddeen Abbas a majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel