Majalisa Ta 10: Peter Obi Ya Bayyana Zabinsa a Kujerar Shugabancin Majalisa

Majalisa Ta 10: Peter Obi Ya Bayyana Zabinsa a Kujerar Shugabancin Majalisa

  • Rahotanni daga ɓangaren jam'iyyar Labour Party sun bayyana zaɓinsu a shugabancin majalisar dattawa da majalisar wakilai
  • Haka kuma, an tattaro cewa an gudanar da taro akan hakan wanda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, ya halarta
  • Abinda aka tattauna a taron ya nuna jam'iyyar ta buƙaci ƴan majalisunta su goyi bayan Sanata Abdulaziz Yari da Hon. Muktar Aliyu Betara

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya bayyana ƴan takararsa a kujerar shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai.

Jaridar Guardian ta kawo rahoto cewa Peter Obi, ya yi zama da zaɓaɓɓun ƴan majalisar jam'iyyar LP a birnin tarayya Abuja, kafin zuwan ranar da za a ƙaddamar da majalisa ta 10.

Peter Obi ya bayyana zabinsa a shugabancin majalisa
Peter Obi ya gana da 'yan majalisar LP inda ya gaya musu wanda za su zaba Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Sai dai, mambobin jam'iyyar Labour Party sun bayyana cewa an umarce su da su zaɓi Sanata Godswill Akpabio a shugabancin majalisar dattawa da Muktar Betara a kujerar kakakin majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Masu Neman Shugabancin Majalisa, Bayanai Sun Fito

Da ya ke tabbatar da hakan, wani mamban jam'iyyar wanda da shi aka yi zaman tare da Peter Obi ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tun da farko mun zauna da Datti kafin yanzu, inda ya gaya mana cewa ba zamu iya zaɓar Tajudeen Abbas, Akpabio ko wani ɗan takara da APC ta ke marawa baya ba."
"Ya gaya mana cewa APC ta marawa Abbas baya ne domin a rage masa ƙarfi sannan ta marawa Benjamin Kalu baya ne domin ya rage ƙarfin Alex Otti a jihar Abia. An tashi taron wanda aka yi a Chopsticks ba matsaya."

Peter Obi ya umarci su zaɓi Yari da Betara

Majiyar ya kuma bayyana cewa an gudanar da wani taron a wani waje daban, wanda Peter Obi ya halarta.

Ya tabbatar da cewa Obi ya buƙace su da su zaɓi Sanata Abdul’aziz Yari, a kujerar shugaban majalisar dattawa. A ɓangaren kakakin majalisar wakilai kuma Obi ya buƙace su da su zaɓi Muktar Aliyu Betara.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Kamar yadda Vanguard ta rahoto majiyar ya bayyana cewa:

"An gudanar da wani taron a ranar Litinin da misalin ƙarfe 5 na yamma. Obi ya halarci zaman. Ya bayyana cewa yana goyon bayan Yari a shugabancin majalisar dattawa da Betara a shugabancin majalisar wakilai. Ya kuma umarci dukkanin zaɓaɓɓun ƴan majalisar LP su zaɓi Betara da Yari."

Tinubu Ya Zabi Akpabio

A baya rahoto ya zo kan cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya marawa tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio baya a shugabancin majalisar dattawa.

Shugaba Tinubu ya kuma marawa Sanata Barau Jibrin baya ya zama mataimakin Akpabio.

Asali: Legit.ng

Online view pixel