Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Masu Neman Shugabancin Majalisa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Masu Neman Shugabancin Majalisa, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu daga cikin ƴan takarar da ke neman shugabancin majalisar wakilai ta 10
  • Shugaban ƙasar ya gana da biyar daga cikin ƴan takarar masu adawa da zaɓin da jam'iyyar APC ta yi kan shugabancin majalisar
  • An hango tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa a Villa

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanya labule da wasu daga cikin ƴan majalisar da ke neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta 10, rahoton Tribune ya tabbatar.

Daga cikin ƴan majalisar da shugaban ƙasan ya sanya labule da su sun haɗa da, Yusuf Gadgi, mai wakiltar Pankshin/Kanke a jihar Plateau, Sada Soli, mai wakiltar Jibia/Kaita a jihar Katsina.

Tinubu ya sanya labule da masu neman shugabancin majalisa
Shugaban Tinubu ya gana da wasu masu neman shugabancin majalisa Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Sauran sun haɗa da Miriam Onuoha, mai wakiltar Okigwe ta Arewa da Muktar Betara, mai wakiltar Biu/Bayo/Shani/Kwayar Kusar a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mambobi Sun Zaɓi Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi da Mataimakinsa

Shugaban ƙasar ya kuma sanya labule da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase, wanda yana ɗaya daga cikin masu neman kujerar kakakin majalisa ta 10.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zaman na su ya samu halartar shugabancin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ciki har da sakataren jam'iyyar na ƙasa Sanata Iyiola Omisore.

Shugabancin majalisa na ba APC ciwon kai

Duk da dai cikakkun bayanai ba su gama fitowa ba dangane da zaman da shugaban ƙasar ya yi da ƴan takarar, zaman na su baya rasa nasaba da batun rikicin shugabancin majalisar.

Jam'iyyar APC da shugaba Tinubu sun zaɓi Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu, a matsayin ƴan takararsu a kujerar kakakin majalisae wakilai ta 10. Wannna zaɓin na su dai ya fusata sauran ƴan takarar da ke neman kujerar.

Akwai yiwuwar shugaba Tinubu ya nemi shawo kan ƴan majalisar su zo su marawa ɗan takararsa baya a kujerar shugabancin majalisar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali Yayin Da Aka Samu Kakakin Majalisa Guda Biyu a Jihar Nasarawa

Shugaba Tinubu ya kuma sanya labule da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje da kuma shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.

Yari Ya Ziyarci Buhari Kan Shugabancin Majalisa

A wani rahoton na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Yari ya je wajen Buhri ne neman sa albarka kan kudirinsa na zama.shugaban majalisar dattawa ta 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel