Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

Shugabancin Majalisa: Cikakkun Bayanai Kan Ziyarar Yari Wajen Buhari a Daura Sun Bayyana

  • Sanata Godswill Akpabio na jihar Akwa Ibom, ka iya fuskantar ƙalubale fiye da yadda ake tunani a takararsa ta shugabancin majalisar dattawa
  • A yanzu haka akwai masu ƙulle-ƙullen tuntsirar da Akpabio a zaɓen, duk da kasancewarsa ɗan takarar da jam’iyyar APC mai mulki ta tsaida
  • Cikin ‘yan kwanaki kaɗan da suka rage a ƙaddamar da majalisar ta ƙasa ta 10, Sanata Abdulaziz Yari na ƙara samun karɓuwa da farin jini

Katsina , Daura - Wani rahoto da ya fito ya tabbatar da cewa Sanata Abdulaziz Yari ya kai ziyara garin Daura jihar Katsina, tare da rakiyar wasu sanatoci.

An ce Yari ya kai ziyarar ne domin neman sa albarkar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kan aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa, ta samu nasara.

Idan dai za a iya tunawa, a baya rahotanni da dama sun nuna cewa, tsohon shugaban ƙasar ya ƙi amincewa da buƙatar Yari, inda ya ce masa ya mutunta hukuncin da jam’iyyar APC ta yanke, na ayyana Sanata Godswill Akpabio a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Kotun Sauraren Kararrakin Zabe: Cikakken Jerin Jihohin Da Peter Obi Ke Kalubalantar Sakamakon INEC

Abdulaziz Yari ya kai wa Buhari ziyara a Daura
Buhari ya yi wa Abdulaziz Yari kyakkyawar tarba a ziyarar da ya kai masa. Hoto: Abdulaziz Yari
Asali: UGC

A halin da ake ciki kuma, an tattaro cewa tsohon shugaban ƙasar, ya tarbi Yari ne jim kaɗan bayan da wasu zaɓaɓɓun sanatoci na majalisar wakilai ta 10 mai zuwa suka amince da goya masa baya a takararsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanatoci da dama ne suka raka Yari zuwa wajen Buhari

Legit.ng ta tattaro cewa, kimanin zaɓaɓɓun sanatoci 22 ne daga jam’iyyu daban-daban suka raka Yari a ziyarar tasa domin taya tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, murnar kammala mulkinsa lafiya.

Wata majiya daga cikin mahalarta ganawar ta Yari da Buhari ta ce:

“Tawagar ta samu kyakkyawar tarba daga wajen tsohon shugaban ƙasa Buhari cikin raha. Taron ya yi armashi sosai kuma tawagar ta tabbatarwa da tsohon shugaban ƙasar cewa ba suna fito na fito ba ne, kawai dai sun himmatu ne wajen karfafa bangaren majalisa.”

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Abdul'aziz Yari Ya Samu Gagarumar Nasara a Kotu Dab Da Zaben Shugaban Majalisa

“Ko kaɗan shugaba Buhari bai yi wani tsokaci na nuna rashin amincewa ba. Ku tuna cewa a lokacin da yake shugaban ƙasa, ya ba majalisa ‘yancin cin gashin kanta, kuma ya zama dole a ɗore a irin wannan tsarin a halin da ake ciki yanzu, wannan shi ne ainihin dimokuradiyya.”

Buhari ya ce a gayawa 'yan Najeriya yana nan cikin ƙoshin lafiya

Majiyar ta kuma bayyana cewa shugaba Buhari ya ji dadin ziyarar inda cikin raha ya bayyana cewa, ya kamata su gaya wa ‘yan Najeriya cewa yana nan cikin koshin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa Yari na da goyon bayan mafi yawan zaɓaɓɓun sanatoci, ciki har da manyan ‘yan majalisu a jam’iyyar APC da ma na sauran jam’iyyu gabanin ƙaddamar da majalisar ta 10, inda zaɓaɓɓun sanatoci za su zaɓi shugaban majalisar dattawan.

Sanata Yari dai zai fafata ne da tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio a takarar shugabancin majalisar dattawan.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Buhari Ya Yi Watsi Da Kudirin Yari Da Kalu Na Shugabancin Majalisa, Ya Bayyana Kwararan Dalilansa

An bayyana abubuwan da za su taimaki Tinubu a mulkinsa

Wani labarin da Legit.ng ta kawo, wata jagora a jam'iyyar APC mai mulki, Adaku Ogbu-Aguocha, ta faɗawa sabon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, abubuwan da zai yi domin samun nasarar gudanar da mulkinsa.

Adaku, wacce 'yar takarar sanata ce a jihar Enugu, ta bayar da shawarar ne a lokacin da take taya sabon shugaban ƙasar murnar fara mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel