Rusau: Kwamishinan Ganduje Ya Mayarwa Abba Martani Kan Asibitin Yara Na Hasiya Bayero

Rusau: Kwamishinan Ganduje Ya Mayarwa Abba Martani Kan Asibitin Yara Na Hasiya Bayero

  • Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Ganduje, Muhammad Garba ya mayar da martani kan raɗe-raɗin da ake cewa sun siyar da asibitin Hasiya Bayero
  • Ya ce sauya masa guri aka yi, sannan kuma an bar ginin na asibitin ya zama cibiyar kula da yara masu cutar ƙarancin abinci a jiki da aka fi sani da tamowa
  • Kwamishinan ya kuma ce har zuwa ranar da Ganduje ya sauka daga mulki, ba a siyar da asibitin ba kamar yadda wasu ke iƙirari, yana nan a matsayin mallakin gwamnatin Kano

Kano - Gwamnatin Kano da ta shuɗe ta mayar da martani game da rusa gine-gine da gwamnati mai ci ta Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ke yi a cikin 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na gwamnatin Ganduje, Muhammad Garba a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce an yi wa ubangidansa mummunar fahimta ne game da batun asibitin yara na Hasiya Bayero.

Kwamishinan Ganduje ya mayarwa da Abba Gida Gida martani
Kwamishina ya ce Ganduje bai siyar da asibitin Hasiya Bayero ba. Hoto: Gida-Gida TV
Asali: Facebook

Ganduje ya mayar da asibitin zuwa cibiyar kula da ciwon tamowa

Tsohon kwamishinan ya ce an dakatar da ayyukan asibitin na wani ɗan lokaci ne bayan kammala aikin asibitin yara na Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu, ɗaya daga cikin ayyukan da gwamnatin Ganduje ta gada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sabon asibitin ƙananan yaran wanda ya fi wancan yawan gadaje, a yanzu yana samar da ingantattun ayyuka baya ga cibiyar horar da ma'aikata da kuma ayyukan bincike da ke ciki kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Muhammad ya yi nuni da cewar an yi shawarar mayar da tsohon asibitin Hasiya Bayero zuwa cibiyar kula da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da aka fi sani da tamowa, wanda zai zama cibiyar kula da cutar.

Kara karanta wannan

Malamin Addini Ya Ci Gyaran Abba Gida-Gida, Ya Fadi Yadda Gwamna Zai Karbe Fili

Kwamishinan ya ƙara da cewa, baya ga haka, akwai tsarin samar da wata masana’anta da za a riƙa haɗa abincin maganin na tamowa a cibiyar da ma a sauran cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar.

Ganduje bai siyar da asibitin na Hasiya Bayero ba

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Ganduje ta ƙaddamar da wani kwamiti da zai sa ido a kan yadda za a aiwatar da aikin, wanda aka tura ya yo rangadin a wani wuri makamancin wannan da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Kwamishinan ya ce, har zuwa ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara, ba a sayar da wurin ga wani ko wata ƙungiya ba, wurin yana nan a matsayin mallakin gwamnatin jihar Kano, kamar yadda ya zo a rahoton The Sun.

Halartar bikin rantsar da Abba Gida Gida ta sa PDP rasa babban jigonta

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun ji yadda jam'iyyar PDP reshen jihar Jigawa, ta yi asarar wani babban jigonta sakamakon halartar bikin rantsar da Abba Gida Gida da ya yi makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Yi Rusau, Abba Gida Gida Zai Koma Kan Masu Satar Kaya da Sunan Ganima

Alhaji Aminu Jahun, jigo a jam'iyyar PDP ta jihar Jigawa ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar biyo bayan dakatarwa da aka yi masa na tsawon wata guda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel