Halartar Rantsar Da Abba Gida Gida Ya Yi Sanadin Fitar Jigon PDP Daga Jam'iyya

Halartar Rantsar Da Abba Gida Gida Ya Yi Sanadin Fitar Jigon PDP Daga Jam'iyya

  • Babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa PDP, ta rasa ɗaya daga cikin jiga-jiganta a jihar Jigawa zuwa wata jam’iyyar
  • Alhaji Aminu Nuhu Jahun, wani jigo a jam’iyyar PDP ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne sakamakon dakatarwar da jam’iyyar ta yi masa
  • Jam’iyyar PDP reshen Jigawa ta dakatar da Jahun ne bayan halartar bikin rantsar da Gwamnan Kano, Abba Gida-Gida

Dutse, Jigawa - Alhaji Aminu Nuhu Jahun, babban jigo a jam’iyyar PDP ta yankin arewa maso yamma, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Ficewar tasa ta biyo bayan dakatarwar da kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ya yi masa na tsawon wata ɗaya.

Babban jigo Aminu Jahun ya fice daga jam'iyyar PDP
Jigo a jam'iyyar PDP reshen Jigawa ya bayyana dalilan ficewarsa daga jam'iyyar. Hoto: Abba Alhaji Garba, Saidu Dan Alhaji
Asali: Facebook

Halartar bikin rantsar da Abba ne ya janyo masa matsala

Wani jami’in jam’iyyar PDP na ƙasa, ya tabbatar da ficewar Jahun ɗin tare da yin ƙarin haske kan halin da ake ciki dangane da dakatarwar da aka yi masa, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Zabo Malamin Makarantar Firamare a Matsayin Dan Takarar Mataimakin Gwamna a Jihar Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban dalilin da ya janyo dakatarwar ta Jahun shi ne, halartar taron rantsar da Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Kano, na jam'iyya mai alamar kayan marmari, NNPP.

Jahun ya ce kwamitin ayyuka na jam'iyyar ta PDP reshen jihar Jigawa, sun gayyace shi zuwa ofishinsu, sannan suka bijiro masa da batun zuwa rantsar da Abba Gida-Gida da ya yi.

Ya ƙara da cewa bayan ya bar wurin ne aka aiko masa da takardar dakatarwa daga jam'iyyar daga baya.

Jahun ya ce bai karya wata doka ba

Jahun ya ce shi bai karya wata doka ba na halartar bikin rantsar da Abba Gida-Gida da ya yi, inda ya ƙara da cewa ko gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ne ya gayyacesa to lallai zai amsa gayyatar.

Ya kuma bayyana irin tsawon lokacin da ya ɗauka yana hidimtawa jam'iyyar ta PDP, sannan ya buƙaci mutane su riƙa bambancewa tsakanin ra'ayin siyasa da kuma na ƙashin kan mutum.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bayanai Sun Bayyana Yayin da Atiku, Makinde Da Magajin Wike Suka Sa Labule

Muƙamai biyar da bai kamata Tinubu ya bai wa 'yan siyasa ba

A wani labarinmu na baya, kun ji cewa an shawarci sabon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan wasu muƙamai da bai kamata ya hannanta ga 'yan siyasa ba.

Daniel Bwala, hadimin ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya bai wa Tinubu wannan shawara a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel