Malamin Addini Ya Ci Gyaran Abba Gida-Gida, Ya Fadi Yadda Gwamna Zai Karbe Fili

Malamin Addini Ya Ci Gyaran Abba Gida-Gida, Ya Fadi Yadda Gwamna Zai Karbe Fili

  • Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi magana a kan yadda sabon Gwamnan jihar Kano yake ruguza gine-gine
  • Malamin addinin Musuluncin ya ce Gwamna zai iya karbe filin mutum, amma a sai an bi wasu matakai tukun
  • Baristan ya nuna kyau Abba Kabir Yusuf ya sanar da jama’a, kuma ya biya su kudin filinsu kafin a ruguza

Kano - A halin yanzu, sabon Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya dauko rushe-rushen gine-ginen da ya kira wanda ya saba doka da tsarin taswira.

Rushe-rushen da ake yi sun jawo surutu a gida da wajen Kano, daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu har akwai Sheikh Ishaq Adam Ishaq.

Ishaq Adam Ishaq wanda masanin shari’ar kasa ne ya yi bayanin da tamkar gyara ne da sabuwar Gwamnatin da aka rantsar a karshen Mayu a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Yi Rusau, Abba Gida Gida Zai Koma Kan Masu Satar Kaya da Sunan Ganima

Malamin Addini Ya Ci Gyaran Abba Gida-Gida
Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan Rabiu Kwankwaso Hoto: @Ibraheemz01
Asali: Facebook

Ganin ana ruguza gidaje da kadarorin al’umma, a wani karatu da malamin ya yi wanda aka gutsuro bangarensa a Twitter, ya yi kira ga mahukunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin ya ce kyau duk abin da shugaba zai yi, ya bi ka’idar da dokar kasa da tsarin mulki ya tsara, sannan ya soki gwamnatocin da aka rika yi a baya.

Sheikh Ishaq Adam ya ce bangarori na 28, 51 da 48 na dokar filaye ta 1978 sun yi bayanin hanyoyin da za a bi wajen karbewa wani filin da aka ba shi.

Bayanin da Shehi ya yi a karatu

"Duk abin da shugaba zai yi, to ya yi shi a kan ka’ida. Yanzu ka ga idan mu ka duba Kano, mun tashi ana ta rusau.
Ba laifi ba ne Gwamna ya karbe fili, har masallacin nan Gwamna zai iya karbe shi, zai iya zuwa ya ce na karbe shi.

Kara karanta wannan

Kamfani Ya Maka Gwamnatin Abba a Kotu, Yana Neman N10bn Saboda Ruguza Otel

Saboda dokar amfani da kasa ta ba Gwamna duk wani iko da fili, shi yake da damar ta-cewa da shi, wannan shi ne doka.
Amma idan an ba ka fili ya zama na ka, watakila ka yi gini ko ka yi wani abin, idan gwamnati ta na son karba, doka tayi bayani.
Na farko dai akwai sanarwa, dole sai an sanar da mutum bisa dokar filaye. Kuma ana karbar fili ne ta hanyoyi biyu kacal.
Ko dai amfanin al’umma ya zarce amfanin daidaikun mutane, ya zama za ayi wani abin da ya shafi bukatar mutane a filin.
Bayan an sanar da mutum, sai a biya shi kudi ta hanyar mallaka masa wani filin ko kuwa kudi, da wannan ake karbar fili.

Ramuwar gayya a Kano?

Malamin yake cewa hanya ta biyu ta karbar fili ita ce idan mutum ya saba sharadin da aka gindaya wajen bada filin, ya ce bai dace a rika bita-da-kulli ba.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Abba Gida Gida Ya Cigaba da Rusau, Ya Ruguza Ginin Otel a Kano

A bidiyon, za a ji malamin ya na zargin Gwamnoni da yin rashin adalci wajen rabon filaye, ya ce wasu sun rika bada filaye masu kyau ga iyalansu a Kano.

Za ayi shari'a a kotu

Tun a baya an ji labari mutane sun fara tsoma baki a kan irin ruguza wurare da Gwamnatin Abba Kabir Yusuf take yi, an ji labari wasu sun tafi kotu.

Kamfanin Lamash Property Ltd ya shigar da kara, ya bukaci a biya sa N10bn domin an jawo masa asara a sakamakon ruguza wani bangare ne Daula otel.

Asali: Legit.ng

Online view pixel