Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

  • Majalisar dattawan Najeriya ta ce ma’aikatun gwamnati sun karbi bashi, amma har yau ba su biya ba
  • An zargi Akanta Janar da sakacin bin wadannan ma’aikatu domin ya karbo bashin kudin da aka ci
  • Binciken kwamitin Matthew Urhoghide ya nuna an karbi Naira biliyan 910, har yau babu labarinsu

Abuja - Majalisar dattawa ta zargi ofishin Akanta Janar na kasa da kin biyan bashin da aka ba ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya.

Rahoton da jaridar Vanguard ta fitar a farkon makon nan ya tabbatar da cewa adadin bashin kudin daga wasu asusu na musamman ya kai Naira biliyan 910.

Shugaban kwamitin da ke kula da baitul-mali, Matthew Urhoghide ya jagoranci binciken bayan dogara da bayanan mai binciken kudi na Najeriya.

majalisa
Shugabannin majalisa a bakin aiki Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Urhoghide mai wakiltar Edo ta kudu a majalisar dattawa ya ce bashi da aron kudin da ma’aikatun gwamnati su ka karba ya kai N910,039,557,742.

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Taurin bashi a gwamnati

Da aka bibiyi lamarin, sai aka gano har zuwa shekarar bara ba a biya wadannan kudi ba, duk da an yi yarjejeniya ba za a dauki lokacin wajen biyan bashin ba.

Jaridar ta ce Ofishin Akanta Janar ya wanke kan shi, ya ce sun aika wasiku barkatai ga Ministar kudi ta lokacin domin ta cirewa MDA bashin da ake binsu.

Akanta Janar ya yi ikirarin tun shekarar 2017 ya so a cire kudin nan da za a biya bashi.

Kwamitin Urhoghide’ ya kuma lura an rika fitar da kudi da sunan ayyuka na musamman, don haka aka ba sabuwar Akanta Janar umarni ta karbo kudin.

Ana sa ran cewa nan da kwanaki 60 za a dawo da wannan bashi da aka karba zuwa baitul-mali. Jaridar Blueprint ta fitar da rahoton a farkon makon nan.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Mai: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC Ta Fadi Bukatunta

Za a binciki SUBEB

Ana haka sai aka ji majalisar dattawan kasar ta bukaci shugaban SUBEB na reshen Imo ya biya duk wasu kudin kamfanonin da ke hannun hukumar.

Shugaban majalisar da ke sa ido kan aikin hukumar SUBEB bai je gaban Sanatocin domin kare kan shi ba.

A fara bincike

Za a ji labari kungiyar SERAP ta roki Bola Ahmed Tinubu ya binciki abin da ya faru a mulkin Muhammadu Buhari, har ta kai ana zargin an tafka badakala.

Ana so sabon shugaban kasa ya kafa kwamitin da zai yi bincike kan bacewar danyen mai tun daga 1999 har zuwa yanzu da aka yi sabon shugaba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel