Yan Bindiga Sun Sheke Mutane 10 a Zamfara, Gwamna Ya Yi Allah Wadai Da Harin

Yan Bindiga Sun Sheke Mutane 10 a Zamfara, Gwamna Ya Yi Allah Wadai Da Harin

  • Mutane akalla 10 sun rasa rayukansu yayin da da dama suka samu raunuka a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kauyukan jihar Zamfara.
  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya yi Allah wadai da wannan harin inda ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a jihar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da wasu da dama suka samu raunuka

Jihar Zamfara – ‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 10 a yankunan Sakiddar Magaji da Jankobo a karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara.

A martaninsa, gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare ya yi Allah wadai da harin inda ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a jihar.

Jihar Zamfara
Yan Bindiga Sun Sheke Mutane 10 a Wani Sabon Hari a Jihar Zamfara. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi 4 ga watn Yuni ta tabbatar da faruwan harin inda ta bayyana cewa mutane da dama sun samu raunuka.

Gwamnan jihar ya bayyana alhininsa da yin Allah wadai da harin

Gwamnan jihar, Dauda Lawal ya bayyana harin a matsayin abin takaici da kuma son hargitsa mutanen da basu ji ba basu gani ba, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta nade hannu ta na ganin ana irin wadannan hare-hare ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mai taimaka masa ta fannin yada labarai, Mustapha Jafaru inda yace gwamnatinsu tana iya kokarinta don ganin an kawo karshen hare-haren.

A cewarsa:

"Wannan harin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ke aiki tukuru don samun hanyoyin dakile matsalolin tsaro a jihar.
“An ba da umarni ga shugabannin tsaro daban-daban a jihar da su tura jami’an tsaro cikin gaggawa yankunan da abin ya faru don dakile faruwar harin a nan gaba.”

Gwamnan ya taya iyalan wadanda abin ya rutsa da su alhini inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a harin, cewar Punch.

Rundunar soji sun kuma hallaka 'yan bindiga biyar

A wani rahoton, rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga biyar da suka addabi wasu yankuna a jihar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an tsaro da aka tura yankin sun samu bayanan sirri cewa ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Rogoji a karamar hukumar Bakura da kuma kauyen Sakiddar Magaji a yankin Janbako a karamar hukumar Maradun da ke jihar.

‘Yan Bindiga Sun Yi Alkawarin Cigaba da Kashe-Kashe a Zamfara

A wani labarin, 'yan bindiga a jihar Zamfara sun yi alkawarin ci gaba da kai hare-hare a jihar.

Wasu mazauna garin Birnin Magaji a jihar Zamfara sun tabbatar da cewa 'yan bindiga da suka addabesu sun ce dole sai sojoji sun bar yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel