Ganduje Ya Shiga Uku, ‘Yan Takara 15 Sun ba Abba Shawarar a Binciki Tsohon Gwamna

Ganduje Ya Shiga Uku, ‘Yan Takara 15 Sun ba Abba Shawarar a Binciki Tsohon Gwamna

  • Wasu da su ka nemi takara a jam’iyyar PRP a zaben 2023 su na so a binciki Abdullahi Umar Ganduje
  • Kungiyar ‘yan takaran ta ce akwai bukatar ayi bincike na musamman kan abubuwan da suka faru a baya
  • Dr. Abdullahi UGanduje ya yi shekaru takwas ya na mulkin jihar Kano kafin jam’iyyar NNPP ta ci zabe

Kano - Kungiyar ‘yan takaran jam’iyyar PRP, sun yi kira ga sabon Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya binciki gwamnatin da ta wuce.

A wani rahoto da aka samu daga Daily Trust a ranar Litinin, an fahimci ana neman Abba Kabir Yusuf tayi bincike a kan Abdullahi Umar Ganduje.

A karshen wani taro da aka yi, ‘yan takara 15 da suka nemi mulki a jam’iyyar PDP sun sa hannu, su na rokon a binciki abubuwan da suka faru a baya.

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: Kowa Zai Shiga Duhu, Ma’aikatan Lantarki Za Su Bi NLC Zuwa Yajin-Aiki

Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje a lokacin ya na ofis Hoto: @FAANOFFICIAL
Asali: Facebook

‘Yan takaran nan su na na so ayi bincike a kan yadda aka kashe dukiyar al’umma a lokacin da Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya ke kan mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa za ayi bincike?

Abin da ‘yan takaran su ke so shi ne a gano ko an ci amana ko an yi abin da ya saba dokar aiki.

Baya ga binciken abubuwan da suka wakana tsakanin 2015 zuwa 2023, rahoton ya ce ‘yan takaran sun roki a cigaba da duk wasu ayyukan alheri a Kano.

‘Yan siyasar sun bukaci gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ajiye adawar siyasa a gefe, ta tabbatar da ganin dorewar manufofin da za su amfani mutane.

Murna ga sababbin shiga ofis

Kungiyar ta ‘yan takaran da suka nemi kujera a zaben 2023 tayi amfani da wannan dama, ta taya Mai girma Abba Kabir Yusuf murnar rantsar da shi.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Afkawa Mutane Yayin Jana'iza A Sokoto, Sun Bindige Da Dama

Haka zalika ‘yan takaran sun taya sauran wadanda aka rantsar a karkashin wasu jam’iyyun murna.

A karshe an yi kira ga sabuwar gwamnatin NNPP ta fito da tsare-tsare da manufofi da za su bunkasa harkokin gona da kasuwanci, a samu aikin yi.

Duk da ta taya sabon gwamna murnar hawa kan mulki, kungiyar ta ce za ta rika bin matakan da suka dage wajen yin suka a inda suka ga ba daidai ba.

Ana yin rusau a Kano

An samu labari Gwamnatin jihar Kano ta cigaba da rushe wasu gine-ginen da aka yi a inda ta ke cewa filayen gwamnati ne, kuma an sabawa ka'ida.

Ba da dadewa ba aka ji an rushe ginin da aka yi a Otal ɗin Daula. An yi rushe-rushen ne bayan Mai girma Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel