Jami'an Yan Sanda Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar Filato

Jami'an Yan Sanda Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar Filato

  • Jami'an rundunar 'yan sanda sun sake komawa sun mamaye zauren majalisar dokokin jihar Filato da safiyar Laraba
  • Ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Jos ta kudu ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a Jos, babban birnin Filato
  • Ya ce sun zauna jiya Talata amma suka wayi gari 'yan sanda sun kwace zauren da safiyar Laraba

Jos, Plateau State - Jaridar Punch ta rahoto cewa an sake shiga yanayin tashin hankali da ɗar-ɗar a zauren majalisar dookin jihar Filato, Arewa ta Tsakiya, da safiyar Laraba.

Hakan ya biyon bayan ganin dakarun rundunar 'yan sanda reshen jihar sun mamaye zauren majalisar kuma sun kwace iko sun hana mambobi shiga.

Zauren majalisar dokokin Filato.
Jami'an Yan Sanda Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar Filato Hoto: punchng

Mamban majalisar dokokin jihar, Honorabul Gwottson, mai wakiltar mazaɓar Jos ta kudu ne ya tabbatar da faruwar haka ga jaridar a Jos, babban birnin jihar Filato.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗau Zafi, Ya Ce Zai Soke Lasisin Mallakar Duk Gidan Man da Ya Ɓoye Fetur Ko Ya Kara Farashi

Gwottson, wanda ya yi allah wadai da matakin dakarun 'yan sandan, ya ce lamarin ya hana mambobin majalisa taruwa domin ci gaba zama kamar yadda suka tsara yau Laraba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da yake kokawa kan wannan yanayi da suka tsinci kansu a majalisa, ɗan majalisar ya ce:

"Mun yi zama jiya (Talata) ba tare da wata matsala ba kuma mun duba wasu muhimman kudirori, muka amince da wasu domin walwalar al'umma."
"Mun tsara zamu dawo yau (Laraba) mu ƙara zama domin ci gaba da ayyukan mu na ɓangaren masu doka, ba zato jami'an 'yan sanda suka mamaye zauren."
"A matsayin na yan majalisa bamu san wani dalili da yasa yan sanda suka sake kwace zauren majalisa a karo na biyu ba, suka hana mambobi sauke nauyin da ke kansu."

Mista Gwottson ya ƙara da cewa zasu kira taron menama labarai nan ba da jimawa ba domin jawo hankalin duniya kan abinda ke faruwa a jihar Filato saboda yan sanda na kokarin kashe demokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jim Kaɗan Bayan Rantsuwa, Gwamna Arewa Zai Ɗauki Matasa 20,000 Aiki

Idan baku manta ba, jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokokin Filato watanni biyu da suka shiga har suka garkame zauren da kwado, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tun wancen lokacin mambobin majalisar ba su samu ikon zama ba sai jiya Talata 30 ga watan Mayu, 2023, awanni 24 bayan rantsar da sabon gwamna, Caleb Mutfwang.

Ta Tabbata, Gwamnatin Tinubu Ta Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin Najeriya ta fitar da sabon farashin litar man Fetur bayan cire tallafin da take ware wa.

Magana ta tabbata, Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin Man Fetur, NNPC ya fara siyar da lita kan sabon farashi.

Bincike ya nuna gidan man NNPC Limited ya sauya farashi a Abuja, Legas da Patakwal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel