Gwamna Bala Muhammed Zai Dauki Matasa 20,000 Aikin Tsaro a Bauchi

Gwamna Bala Muhammed Zai Dauki Matasa 20,000 Aikin Tsaro a Bauchi

  • Gwamnatin Bauchi zata ɗauki matasa 20,000 aiki a hukumar tsaron da zata kafa mai sumfurin Amotekun
  • Gwamna Bala Muhammed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan ranstuwar kama aiki a matsayin gwamna zango na biyu
  • Ya ce ba zai yuwu wasu baƙin yan bindigan jeji su shigo su hana al'ummar da suka zaɓe shi zaman lafiya ba

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ta fara shirye-shiryen ɗaukar ma'aikata matasa aƙalla 20,000, waɗanda za'a ba su horo a matsayin dakarun rundunar tsaro ta jiha.

Tribune ta ce gwamnatin zata ɗauki wannan mataki ne a yunkurin magance matsalar tsaro, samar da ayyukan yi, da dawo da zaman lafiya da aminci tsakanin al'ummar Bauchi.

Gwamna Bala Muhammed.
Gwamna Bala Muhammed Zai Dauki Matasa 20,000 Aikin Tsaro a Bauchi Hoto: Sen Bala Abdulkadir Muhammed
Asali: Facebook

Matasan da gwamnatin zata ɗauka zasu shiga ɓangaren gidauniyar kafa hukumar tsaro ta jiha wacce zata yi shigen dakarun Amotekun na Kudu Maso Yamma.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Gabatar da Muhimmiyar Buƙata Ga Gwamnatin Tarayya Ana Gab da Rantsar da Tinubu

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed Abdulkadir, ne ya tabbatar da haka jim kaɗan bayan ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamna zango na biyu tare da mataimakinsa, Mohammed Auwal Jatau.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wane aiki matasan zasu yi wa gwamnatin Bauchi?

A cewar mai girma gwamna, rundunar jami'an tsaron wanda ya raɗa wa suna, "hukumar 'yan banga da tallafawa matasa," suna da sumfuri iri ɗaya da na hukumar Amotekun.

Ya cewa hukumar tsaron zata taka rawa wajen daidaita al'amura da tsare-tsaren samar da tsaro waɗanda tuni aka kafa a kananan hukumomin da ke faɗin jihar Bauchi.

A kalamansa ya ce:

"Hukumar tsaron zata saita tsarukan da muka gina na tabbatar da tsaro a matakin kananan hukumomi. Zamu ɗauki matasa 20,000 a rukunin farko na shirin."
"Babu tantama 'yan banga su na ba da muhimmiyar gudummuwa wajen sa ido kan ɓata garin da suka hana mutanen kauye zaman lafiya da nufin raba su da mahallansu."

Kara karanta wannan

Canja Fasalin Naira: An Faɗi Matakan da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Gwamnan CBN da Wasu Jiga-Jigai

Rahoton Punch yace Ƙauran Bauchi ya yi gargaɗi da babban murya cewa ba zai zauna ya zuba ido wasu baƙin 'yan fashin daji su shigo Bauchi kana su kwace iko da wasu yankuna ba.

Ya kuma tabbatarwa Sarakunan gargajiya, Malamai da shugabannin al'umma cewa zasu ci gaba da ba da gudummuwa kamar yadda Allah ya ɗora musu nauyin kare rayukan jama'arsu.

Sabon Gwamnan Kano Ya Kori Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai, Ya Maye Gurbinsa

A wani labarin kuma Abba Gida Gida ya kori shugaban hukumar Alhazai, Sheikh Pakistan, ɗiyar marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam daga bakin aiki.

Sabon gwamnan na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sallami baki ɗaya mambobin majalisar gudanarwa na hukumar jin daɗin Alhazai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel