Gwamna Kwara Ga Yan Kasuwa: Duk Wanda Ya Boye Fetur Zan Kwace Lasisinsa

Gwamna Kwara Ga Yan Kasuwa: Duk Wanda Ya Boye Fetur Zan Kwace Lasisinsa

  • Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya roki 'yan kasuwar man Fetur su guji sake jefa mutane cikin wahalar rayuwa
  • A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce duk gidan man da aka kama yana ɓoye man Fetur, zai soke lasisin hakkin mallakarsa
  • Ya ce karancin man da aka kirkiro wani yunkuri ne na karkartar da ma'anar kalaman shugaban kasa, Bola Tinubu

Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a ranar Talata, ya gargaɗi 'yan kasuwan man Fetur su guji jefa mutane cikin sabuwar wahalar ƙarancin Man Fetur.

Gwamna AbdulRazaq, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, ya yi wannan gargaɗi ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa labaransa, Rafiu Ajakaye.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.
Gwamna Kwara Ga Yan Kasuwa: Duk Wanda Ya Boye Fetur Zan Kwace Lasisinsa Hoto: Kwara State Government
Asali: Facebook

Ya ce wannan yanayin haɗi da matakin gidajen mai na daina sayarwa direbobin ababen hawa man Fetur abin takaici ne, inda ya yi kira ga yan kasuwa su saki man Fetur ga kowa.

Kara karanta wannan

"Tallafin Man Fetur Ya Tafi," Shugaba Tinubu Ya Fara Ɗaukar Matakai Masu Tsauri

Gwamnan ya buƙaci masu kasuwancin Mai su buɗe gidan mai nan take kuma su ci gaba da sayarwa mutane a kan farashi tunda gwamnati ba ta ƙara farashin lita ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, man fetur ɗin da yan kasuwan ke da shi yanzun gwamnati ta biya tallafi a kansa, don haka babu dalilin ɓoyewa ko ƙara farashin litar mai, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Sanarwan ta ce:

"Kirkiro karancin Man fetur wata hanya ce ta karkata ainihin abinda kalaman shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ke nufi game da tallafin man fetur. Bai kamata wahalar ta ƙare kan talakawa ba."
"Mai girma gwamna ya roki yan kasuwa su kaucewa abimda da za'a iya kira da zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa. Adana Man Fetur ɗin da kuka siyo kan faracin tallafi zai jefa mutanen Kwara cikin ƙunci kuma ba zamu lamurta ba."

Kara karanta wannan

Canja Fasalin Naira: An Faɗi Matakan da Ya Kamata Tinubu Ya Ɗauka Kan Gwamnan CBN da Wasu Jiga-Jigai

Wane mataki gwamnatin Kwara ta shirya ɗauka?

Sanarwan ta kara da cewa mataimakin gwamna zai jagoranci tawagar jami'an da zasu fita rangadi don tabbatar da babu gidan man da ya ƙara kuntatawa mazauna Kwara.

"Mai girma mataimakin gwamna, Kayode Alabi, zai jagorancin tawagar da zasu tabbatar babu wani ɗan kasuwar man fetur da ya ƙara jefa mutanen Kwara cikin wahalhalu."
"Kowane gidan mai ya sani wannan tawagar zata yi bincike mai zurfi har cikin ramin aje man Fetur kuma duk gidan man da aka gano yana ɓoye mai zai rasa shaidar mallaka da sauran hukunci mai tsauri."

Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Shiga Ofis, Ya Faɗi Gaskiya Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur

A wani labarin kuma Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada shirin gwamnatin shugaba Tinubu na cire tallafin man Fetur.

Shettima ya faɗi haka ne bayan shiga Ofis a Villa da misalin karfe 12:39 na tsakar ranar Talata, 30 ga watan Mayu, 2023 domin fara aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Ta Ayyana Hutun Kwana 1 Saboda Bikin Rantsar da Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel