Ta Tabbata, Gwamnatin Tinubu Ta Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

Ta Tabbata, Gwamnatin Tinubu Ta Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya

  • Bayan dogon lokaci, daga karshe Najeriya ta daina biyan kuɗin tallafin man Fetur a faɗin kasar
  • Kamfanin mai na kasa NNPC Limited ya tabbatar da haka yayin da aka wayi gari ya kara farashin litar mai a sassan Najeriya
  • Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan shugaban kasa, Bola Tinubu, ya ce tallafin mai ya tafi

Abuja - Daga karshe, Najeriya ta cire tallafin man premium motor spirit (PMS) wanda aka fi sani da Man Fetur yayin da kamfanin mai na ƙasa NNPC ya fara siyar da mai a sabon farashi.

Leadership ta tattaro cewa a safiyar ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, kamfanin NNPC Limited ya sauya farashin Man Fetur zuwa N537 kan kowace lita ɗaya a Abuja.

NNPCL.
Ta Tabbata, Gwamnatin Tinubu Ta Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Binciken jaridar ya nuna cewa makamancin haka ne ya faru a jihar Legas, inda gidan mai mallakin kamfanin NNPCL a Titin Ota, Abule-Egba, ya fara siyar da litar mai kan N488.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kungiyar Kwadago Ta Dau Zafi, Ta Yi Watsi Da Sabon Farashin Man Fetur

Haka zalika a gidan man NNPC Mega Station da ke tashar motocin Legas a Patakwal, babban birnin jihar Ribas, litar fetur ta koma farashin N511 da safiyar Laraba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jihar Filato da ke shiyyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya, farashin litar mai ya koma N537 a gidanjen mai mallakin kamfanin NNPC Limited.

Kamfanin NNPCL ne kaɗai ke samar da man Fetur a Najeriya a halin yanzu kuma ana tsammanin sauran 'yan kasuwar mai zasu bi sahu, su koma sabon farashi da safiyar nan.

Ba tallafi kaɗai FG ta cire ba - Masana

A cewar masu nazari kan batun, tunda kamfanin NNPC Limited ya canja farashi kala daban-daban a biranen Najeriya, haka na nufin ba tallafi kaɗai gwamnatin tarayya ta cire ba.

Sun ce tsarin daidaita farashin Fetur zuwa farashin da gwamnati ta kayyaɗe a faɗin Najeriya ma ya tafi tare da tallafin Fetur, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su Shirya, NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur a Duk Gidajen Mai da Ke Karkashinsa

Babu tabbaci kan a wane farashin musanyar kuɗi kamfanin ya ɗauka wajen kayyade saboN farashin amma ana hasashen ba zai wuce kewayen N600 kan ƙowace dala ɗaya ba.

Tsohon Kakakin Buhari Ya Samu Aiki Kwanaki Kadan Bayan Barin Mulki

A wani labarin na daban kuma Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya samu aikin kamfanin jaridar bayan shekara 8.

Tsohon kakakin Buhari ya sanar da samun aiki a tsohuwar jaridar da ya bari lokacin da ya shiga gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel