Kafin Tinubu Ya Gyara Zama a Ofis, Atiku da Obi Sun Cigaba da Shirin Karbe Mulki a Kotu

Kafin Tinubu Ya Gyara Zama a Ofis, Atiku da Obi Sun Cigaba da Shirin Karbe Mulki a Kotu

  • Lauyoyin Atiku Abubakar sun tanadi lodin hujjoji daga BVAS da za su gabatar a kotun karar zabe
  • ‘Dan takaran na PDP ya na fatan Alkalan kotun korafin zabe su gamsu cewa APC tayi magudi a 2023
  • Shi ma Peter Obi ya ci aniyar tsige Bola Tinubu, ya fadawa kotu an taba kama shi a harkar kwayoyi

Abuja - A ranar Talata, Atiku Abubakar ya shiga kotu da tulin takardu da zai gabatar a matsayin hujjoji a shari’ar da ake yi game da zaben shugaban kasa.

Premium Times ta ce Atiku Abubakar wanda ya yi takara a PDP, ya na kokarin gamsar da kotu cewa Bola Tinubu ya yi nasara ne bayan saba dokar zabe.

Atiku da jam’iyyarsa ta PDP mai adawa su na karar Tinubu, Kashim Shettima, APC da INEC.

Bola Tinubu
Bola Tinubu zai zauna a ofis Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A zaman da aka yi a jiya, lauyoyin jam’iyyar PDP da ‘dan takararta sun kawo hujjojinsu wanda su ka hada da bayanan da aka samu daga na’urorin BVAS.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakamakon da aka samu a BVAS

Lauyan Wazirin Adamawa, Eyitayo Jegede ya gabatar da sakamakon zaben shugaban kasa na jihohi 36 da birnin tarayya da aka samu daga na’urar.

Rahoton ya ce Jegede SAN ya kuma gabatar da katin PVC ga Haruna Tsammani da sauran Alkalan da ke sauraron shari’ar, kotu ta yarda ayi hujjar da su.

Lauyoyi masu bada kariya Wole Olanipekun (Tinubu), Lateef Fagbemi (APC) da Abubakar Mahmoud (INEC) ba su nuna su na da wata ja a gabar nan ba.

A karshen zaman, Alkalan sun yanke shawarar a daga karar sai zuwa yau Laraba, a cigaba.

Peter Obi v Bola Tinubu

A rahoton The Cable, an ji kotun sauraron korafin zaben ta karbi shaidan farko (Lawrence Nwakaeti) da Jibrin Okutekpa ya gabatar a madadin LP.

Nwakaeti ya zo ya yi wa kotu bayanin yadda gwamnatin Amurka ta taba karbe $460,000 a hannun Tinubu saboda zargin ya na alaka da miyagun kwayoyi.

Lauyan da ya ke kare Tinubu, Wole Olanipekun ya wanke wanda ake tuhuma. Shi kuma Lauyan APC ya ce masu karar ba su da hujja daga ‘yan sanda.

Tinubu ya fara da sa’a kuwa?

Rahoto ya zo cewa Kungiyar ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa sun ce za su taso Bola Ahmed Tinubu a gaba idan har farashin man fetur ya karu a Najeriya.

Daga hawa mulki, sabon shugaban Najeriya ya ce babu maganar tallafin man fetur a gwamnatinsa. Shugabannin kungiyar IPMAN sun ce ba za su yarda ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel