Muhimman Nade-Nade 3 da Ake Sa Ran Tinubu Zai Yi Nan Take Nan Bayan Rantsar da Shi da Kuma Wadanda Zai Nada

Muhimman Nade-Nade 3 da Ake Sa Ran Tinubu Zai Yi Nan Take Nan Bayan Rantsar da Shi da Kuma Wadanda Zai Nada

  • Ana sa ran zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya yi nade-nadensa na farko da suka hada da SGF, shugaban ma’aikata da kuma kakakin shugaban kasa, nan take bayan rantsar da shi
  • Rahotanni sun bayyana cewa Nasir El-Rufai, Aminu Masari, da Atiku Bagudu ne ke hango kujerar SGF, yayin da Femi Gbajabiamila ke neman shugaban ma’aikatan fadar gwamnati
  • An ce Bayo Onanuga da Dele Alake su ne masu neman kujerar kakakin shugaban kasar da za a rantsar Gobe

FCT, AbujaA bisa al’ada, ana sa ran zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai bayyana nadinsa na farko jim kadan bayan rantsar da babban jojin Najeriya (CJN), Mai shari’a Olukayode Ariwoola.

Wadannan nade-nade na gaggawa na da matukar muhimmanci domin tabbatar da gudanar da ayyukan gwamnati cikin sauki yayin da za a jira wasu nade-naden da ke bukatar amincewar majalisar dokokin kasar.

Kara karanta wannan

"Ka Soke Kujerar Karamin Minista": Shugabannin Addinai Sun Jero Abubuwan Da Suke So Tinubu Ya Yi Da Zaran Ya Karbi Mulki

Tinubu zai yi nade-nade bayan rantsar dashi
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a Najeriya | Hoto: Vanguard News
Asali: Facebook

Muhimman nade-naden uku sune kamar haka:

  1. Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF)
  2. Shugaban ma'aikata
  3. Kakakin shugaban kasa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

El-Rufai ko Masari; daya na iya zama SGF, in ji majiya

Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ne ke sa ido tare da daidaita yadda ake aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin tarayya.

Har ila yau, ofishin na aiki a matsayin cibiyar ba da shawara ta gaba a fadar shugaban kasa; yana tafiyarwa da tsara manufofi, daidaitawa, da aiwatarwa; da kuma sanya ido kan Ma’aikatun Tarayya, Cibiyoyi da Hukumomi.

A cewar jaridar Vanguard, gwamnoni uku masu barin gado ne ke hango kujerar SGF; Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Aminu Masari na jihar Katsina da Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan Tinubu

Shugaban ma’aikata na aiki ne a matsayin hadaka tsakanin ministoci da shugaban kasa kuma yana kula da ma’aikatan fadar gwamnati a lokaci guda, don haka shi ke gina dangantakar shugaban kasa da sauran bangarorin gwamnati biyu.

Kara karanta wannan

Mukamai 3 da Ake Sauraron Sabon Shugaban Kasa Ya Nada da Zarar Ya Shiga Ofis

Akwai rahotannin da ke cewa mai yiwuwa a nada kakakin majalisar wakilai mai barin gado Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan Tinubu.

Sai dai jaridar Vanguard ta ruwaito daga majiya cewa, Gbajabimila na fuskantar hamayya sosai wajen yiwuwar zama shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Kakakin shugaban kasa

Kakakin shugaban kasa ne ke kula da harkokin sadarwa na shugaban kasa. Rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar zaban Bayo Onanuga ko Dele Alake a matsayin.

Onanuga yayi aiki a matsayin daraktan yada labarai na tawagar yakin neman zaben Tinubu/Shettima.

Alake ya taba rike kujerar Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru a gwamnatin Tinubu a lokacin da yake gwamnan Legas.

A halin da ake ciki, akwai manyan abubuwa biyar da ke jiran Bola Ahmad Tinubu bayan karbar mulki daga hannun Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel