Fashola, Ahmad Da Sauran Yan Gwamnatin Buhari Da Ka Iya Samun Shiga Gwamnatin Tinubu

Fashola, Ahmad Da Sauran Yan Gwamnatin Buhari Da Ka Iya Samun Shiga Gwamnatin Tinubu

Za a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, lokacin da shugaban kasa Muhammadu zai bar kujerar mulki a hukumance.

A tafiyarsa na zama zababben shugaban kasa kuma shugaban Najeriya, Tinubu ya yi hadaka da manyan masu fada aji na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ma wadanda ba yan APC ba.

Bola Tinubu, Shugaba Buhari da wasu jami'an gwamnati
Fashola, Ahmad Da Sauran Yan Gwamnatin Buhari Da Ka Iya Samun Shiga Gwamnatin Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Abike Dabiri-Erewa
Asali: Twitter

Hakazalika, hadaka tsakanin rusasshiyar jam'iyyar Congress of Progressives Change (CPC), Action Congress of Nigeria (ACN), wasu yan Peoples Democratic Party (PDP), All Nigeria Peoples Party (ANPP), da wasu da dama ne ya haifar da APC gabannin zaben 2015.

Sai dai kuma, tsakanin 2015 da 2023, an samu sauye-sauye, wasu masu biyayya sun janye, an hau sama an rikito kuma hakan ya ritsa da mutane da dama a gwamnatin shugaba Buhari.

Wannan ne dalilin da yasa ba lallai ne Tinubu, wanda ya zuba ido kan duk abun da ke faruwa ya yi aiki da dukkanin yan majalisar Buhari ba idan ya karbi mulkii a ranar Litinin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, akwai yiwuwar zai yi aiki da wasunsu wadanda aka jero a kasan nan:

Babatunde Fashola

Ministan ayyuka da gidaje mai barin gado ya yi aiki a karkashin gwamnatin shugaban kasa Buhari na tsawon shekaru takwas amma a baya ya yi aiki da Tinubu na fiye da lokacin da ya yi da Buhari.

Fashola ya yi aiki a matsayin shugaban ma'aikatan Tinubu lokacin da yake a matsayin gwamnan jihar Lagas sannan ya kuma gaje shi.

A lokacin kamfen dinsa, Fashola ya goya masa baya sannan ya bayar da gudunmawa wajen nasarar Tinubu kuma wannan na iya ba shi dama sosai a gwamnati mai shigowa.

Abike Dabiri-Erewa

Shugabar hukumar da ke kula da yan Najeriya mazauna waje (NiDCOM) na daya daga cikin manyan yan majalisar Buhari da ka iya samun shiga a gwamnatin Tinubu.

Kamar Fashola, Dabiri-Erewa tana daya daga cikin yan ACN kuma yan APC reshen Lagas a gwamnatin Buhari, sannan tsawon shekaru da dama, ta kasance mai biyayya ga zababben shugaban kasar.

Festus Keyamo

Keyamo yana daya daga cikin manyan masu goyon bayan Tinubu a karkashin gwamnatin Buhari, ya kuma kasance babban kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC.

Karamin ministan kwadagon da daukar ma'aikata na iya yin babban kamu a gwamnatin Tinubu saboda biyayyarsa ga zababben shugaban kasar.

Bashir Ahmad

Matashin dan siyasar na Kano na iya samun shiga koda dai baya cikin sansanin Tinubu da ACN a farkon gwamnatin Buhari.

Sai dai, Ahmed ya tsaya tsayin daka gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC da babban zaben 2023.

Adeleke Olorunibe Mamora

Tsohon sanatan Lagas ta gabas shine ministan kimiyya da fasaha mai ci kuma ya kasance tsohon karamin ministan lafiya duk a gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan aka yi la’akari da Lagas da ACN, akwai yiwuwar Mamora ya samu shiga cikin yan majalisar Tinubu da za su yi fice.

Buhari ya kewaya da Tinubu fadar shugaban kasa

A wani labari na daban, gabannin mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nunawa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu wurare a fadar gwamnati.

Buhari ya zagaya da Tinubu jim kadan bayan idar da sallar Juma'a a ranar 26 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel