Tun Yanzu Wasu Kungiyoyi 3 Sun Fito Za Su Yaki Bola Tinubu Kan Cire Tallafin Fetur

Tun Yanzu Wasu Kungiyoyi 3 Sun Fito Za Su Yaki Bola Tinubu Kan Cire Tallafin Fetur

  • Kungiyar NLC a karkashin Kwamred Joe Ajaero ba ta goyon bayan a janye tallafin man fetur a haka
  • Shugabannin kungiyar TUC su na kan wannan ra’ayi, sun ce sai gwamati ta zauna da al’umma tukun
  • Kamar yadda sanarwa ta fito daga bakin Ukadike Chinedu, IPMAN ta ci gyaran sabon shugaban kasa

Abuja - Kungiyar ‘yan kwadago ta kasa (NLC), ta soki maganar da sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi gaggawar yi a kan tallafin man fetur.

A ranar Talata, Vanguard ta ce shugaban kungiyar NLC, Kwamred Joe Ajaero ya fitar da jawabi, ya na sukar yadda sabuwar gwamnati ta jefa mutane a kunci.

Ajaero ya ce bai kamata Bola Tinubu ya furta cewa an yi waje da tsarin tallafin man fetur ba tare da ya zauna da masu ruwa da tsaki tukun a kan harkar ba.

Kara karanta wannan

Iyalina Ba Su Bukatar Dukiyar Najeriya Domin Mu Rayu Inji Mai Dakin Bola Tinubu

Tinubu
Bola Tinubu a Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ba za mu yarda ba - NLC, IPMAN

Shugaban na NLC ya zargi sabon shugaban Najeriya da rashin tausayi, ya ce ya tsumbula al’umma a wahala da zuwansa maimakon cika alkawarinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An rahoto kungiyar NLC ta na cewa za ta yaki matakin, kuma ta na mai kira da a janye shi.

Kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan da ke saida mai ba ta goyon bayan matsayin sabuwar gwamnati, ita ma ta ce ba haka nan kurum za a dauki mataki ba.

Punch ta ce Jami’in hulda da jama’a na IPMAN ta kasa, Ukadike Chinedu ya ce sai gwamnatin Tinubu ta zauna da ‘yan kasuwa tukuna kafin a janye tallafin.

Cif Ukadike Chinedu ya ce su na nan a kan bakarsu na cewa sai an gyara matatu kafin a cire tallafin fetur domin hakan zai jawo mummunan tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu: Muhimman Abubuwa 7 da Aka Tsakura Daga Jawabin Sabon Shugaban Kasa

Wasa ake yi? - TUC

A jawabin da ya fito daga shugaban TUC da sakatarensa, Festus Osifo da Nuhu Toro, kungiyar ‘yan kasuwar ta nuna ba ta kan shafi daya da Bola Tinubu a nan.

Vanguard ta rahoto kungiyar TUC ta na taya sabon shugaban kasar murnar shiga ofis, amma ta ce idan ana maganar kara kudin man fetur ne, a sake nazari.

Osifo da Toro su na tare da takwarorinsu domin sun ce sai an yi zama da masu ruwa da tsaki, sannan duk an cin ma matsaya kafin gwamnati ta dauki mataki.

Bola Ahmed Tinubu ya fara da sa’a?

Labarin da mu ka samu shi ne a garin Abakaliki daga N230, farashin kowace litar fetur ta koma tsakanin N800 zuwa N1200, kasuwar ‘yan bumburutu ta bude.

Wasu Gwamnoni sun fara daukar mataki a kan masu gidajen man da ke rufewa ko kara kudinsu ba tare da hukuma ta canza farashin da ake sayen mai ba tukun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel