Ku Kira Ni da Mallam Namadi Ba Mai 'Girma Gwamna Ba', In Ji Sabon Gwamnan Jihar Arewa

Ku Kira Ni da Mallam Namadi Ba Mai 'Girma Gwamna Ba', In Ji Sabon Gwamnan Jihar Arewa

  • Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci al’umma su rinka kiranshi da Mallam ba mai girma gwamna ba
  • Gwamnan ya fadi haka ne a yayin bikin rantsar da shi a filin wasa na Aminu Kano da ke babban birnin jihar, Dutse
  • Mai Shari’a, Umar Sadiq ne ya rantsar da Gwamna Umar Namadi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu

Jihar Jigawa - Sabon gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi ya bukaci mutane su rinka kiranshi da Mallam Umar Namadi ba ‘Mai Girma Gwamna’ ba kamar yadda ake kiran sauran gwamnoni.

Gwamna Namadi ya fadi haka ne a yayin bikin rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar tare da mataimakinsa, Aminu Usman a filin taro na Aminu Kano da ke Dutse.

Gwaman Umar Namadi
Sabon Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Taron an gudanar da shi ne a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, inda Mai Shari’a Umar Sadiq ya rantsar da shi, cewar jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Matakalar Taron Rantsar da Abba Gida Gida Ta Rushe Yayin Bikin Rantsar da Shi a Kano

Namadi ya yi alkawarin yin mulki tsakani da Allah

Gwamnan ya yi wa mutanen jihar alkawarin yin mulki da gaskiya kuma tsakani da Allah ba tare da nuna bambanci a tsakanin al’umma ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa gwamnan ya kirayi sauran jam’iyyun siyasa da su zo a hada kai don ciyar da jihar gaba.

Namadi ya ce zai yi kokari don ganin ya cika dukkan alkawuran da ya dauka kafin wa’adinsa na farko ya kare.

Ya ce jin dadin al'umma shi ne kan gaba a gwamnatinsa

Ya kara da cewa jin dadin al’umma da kuma tsarin tattalin arziki mai inganci shi ne babban abin da zai sa a gaba, yayin da ya ce zai kawo masu zuba hannun jari don samar da ayyukan yi.

Sauran wuraren da zai fi sanyawa ido akwai harkan lafiya da ilimi da harkar noma da kuma muhalli.

Kara karanta wannan

Cika aiki: Saura sa'o'i ya sauka, El-Rufai ya haramta wata kungiya a Kaduna

Ya koka kan yadda jihar ta fiskanci ambaliyar ruwa a shekarar 2022 inda aka yi asarar rayuka da dama da kuma gidaje da hanyoyi.

A cewarsa:

“Zamu yi kokari mu kare matsalolin muhalli musamman ambaliyar ruwa da ya lalata wurare da dama a shekarar 2022.”

Namadi ya yi alkawarin duba zuwa ga manyan ayyuka, inda ya ce babban birnin jihar, Dutse za ta fi kowace karamar hukuma samun wadannan ayyuka.

A karshe ya godewa tsohon gwamna, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar bisa halartar taron rantsarwar da ya yi.

An Fara Zargin Gwamnan APC Da Yakar Gwamna Mai Jiran Gado

A wani labarin, gwamnan jihar Jigawa ya bayyana cewa bai da wani nufi na yakar sabuwar gwamnati ta Mallam Umar Namadi.

Badaru ya bayyana haka ne a yayin ganawa da Alhaji Ahmad Gerawa lokacin da ya kai masa ziyara.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel