Jam’iyyar APC Ta Na Yunkurin Karbe Kujerar Sanatan da NNPP Ta Samu a Jihar Kano

Jam’iyyar APC Ta Na Yunkurin Karbe Kujerar Sanatan da NNPP Ta Samu a Jihar Kano

  • Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya shigar da kara a kotu a kan zaben kujerar Sanatan tsakiyar Kano
  • ‘Dan takaran ya dauki Lauya da shaidu 30, ya na kokarin karbe nasarar da Jam’iyyar NNPP ta samu
  • AA Zaura ya na zargin cewa da murdiya ne Sanata Rufai Hanga ya doke shi a zaben na 2023 da aka yi

Kano - Abdulsalam Abdulkarim Zaura wanda ya yi wa APC takarar Sanatan Kano ta tsakiya a zaben 2023 ya shigar da kara a kotun korafin zabe.

Daily Trust ta ce Abdulsalam Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani da AA Zaura ya na kalubalantar nasarar da Hukumar INEC ta ba jam’iyyar NNPP.

Lauyan ‘dan takaran, Ishaka Dikko (SAN) ya bukaci kotun sauraron korafin zaben ta karbe nasarar da aka ba Sanata Rufai Hanga a zaben da ya wuce.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kotun Koli Ta Tsaida Ranar Sauraron Shari’ar PDP v Tinubu da Shettima

Jam’iyyar NNPP
Hanga, Yari, Kwankwaso da Sumaila Hoto: @sameer.hanga
Asali: Facebook

Ishaka Dikko (SAN) ya yi ikirarin an sabawa ka’idar zabe sannan ba a bi dokar kasa a wajen zaben Sanatan Kano ta tsakiya da NNPP ta lashe ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce Lauyoyin bangarorin da ake kara watau INEC, jam’iyyar NNPP da ‘dan takaranta sun musanya ikirarin da Lauyan AA Zaura yake yi.

APC za ta kira shaidu 30

Da aka fara shirin sauraron karar a ranar Talata a kotu, Lauyan da ya tsayawa Zaura ya ce zai gayyaci shaidu 30 domin nuna an yi magudin zabe.

Tribune ta ce Lauyan da ya ke kare NNPP da Rufai Hanga, Meshak Ikpe ya fadawa kotu sun tanadi shaidu uku da za su tabbatar da nasararsu.

Abbas Haladu wanda shi ne Lauyan hukumar zabe ta kasa ya ce shaidu biyu za su kira, shi kuma Ibrahim Shekarau zai gayyaci shaida daya rak.

Kara karanta wannan

Ana Binciken ‘Dan Takaran Gwamnan da Ya Kashe N2bn Ya Saye Kuri’u a Zaben 2023

Zaura ya fadawa kotu cewa zai bukaci wanda zai rika fassara masa abubuwan da ake fada daga Ingilishi zuwa Hausa, sauran ba su bukatar tafita.

Bayan an gama sauraron kowane bangare, sai Alkalin kotun ya daga zaman shari’ar zuwa yau Laraba.

Haduwar Kwankwaso da Tinubu

An yi wata ganawar sirrin tsakanin Asiwaju Bola Tinubu da Rabiu Musa Kwankwaso a Birnin Faris, rahoto ya zo cewa jigon na NNPP ya ba APC sharadi.

Arewa maso yamma ta samu mataimakin shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai, Kwankwaso ya nemi APC ta sake duba lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel