Zaman da Kwankwaso Ya Yi da Tinubu a Faransa Zai Iya Canza Siyasar APC da Majalisa

Zaman da Kwankwaso Ya Yi da Tinubu a Faransa Zai Iya Canza Siyasar APC da Majalisa

  • Kwanakin baya aka ji Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kebe da Bola Ahmed Tinubu a kasar waje
  • Ana rade-radin cewa tsohon Gwamnan Kano ya bada sharadin a canza yadda ware kujerun majalisa
  • Arewa maso yamma sun samu kujeru har biyu, an bar ‘Yan majalisar Arewa ta tsakiya a tutar babu

Abuja - A watan Yuni za a rantsar da zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya a Najeriya, alamu na nuna abubuwa sun canza a ‘yan kwanakin nan.

Rahoton Vanguard ya ce zaman da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi da Bola Ahmed Tinubu a Faransa zai iya jawo a canza yadda aka yi kason kujerun.

APC mai mulki ta kebe bangarori da ‘yan takaran da ta ke goyon baya a zaben majalisa.

Tinubu
Bola Tinubu a wajen wani taro Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Bayan an yi haka ne sai zababben shugaban kasa ya sa labule da Rabiu Musa Kwanwaso wanda ya nemi shugabanci a karkashin jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Dubu ta Cika: Sojoji Sun Kwamushe Rikakken Bai Wa ’Yan Bindiga Bayanan Sirri a Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta ce Rabiu Kwankwaso ya bukaci Tinubu ya sake duba yadda aka yi kason, musamman ganin yadda Arewa maso yamma ta samu kujeru biyu.

Jam’iyyar APC ta na goyon bayan yankin da Kwankwaso ya fito ya samu mataimakin shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai.

‘Yan takaran da aka tsaida su ne Sanata Barau Jibrin wanda ya zama Sanatan Kano ta Arewa a 2015 da kuma Hon. Tajuddeen Abbas daga jihar Kaduna.

Kwankwaso ya bada sharadi?

Babu wanda zai iya cewa ga abin da tsohon Gwamnan na Kano ya tattauna da zababben shugaban, amma ana rade-radin akwai batun 'yan majalisa.

Wata majiya ta ce a cikin sharudan da Kwankwaso ya bada shi ne karbe mataimakin shugaban majalisar dattawa daga Kano zuwa Arewa maso tsakiya.

Majiyar ta koka a kan yadda zababben shugaban na Najeriya ya karbi maganar, ya yarda a canza Barau Jibrin da wani Sanata daga Arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Ji Ganduje a Tarho Yana Kokawa Kan Zaman Tinubu da Kwankwaso a Faransa

Idan labarin ya tabbata, wanda ake tunanin jam’iyyar APC za ta dawo ta marawa baya shi ne Sanata Sani Musa mai wakiltar Neja ta gabas a majalisa.

Hanan a Instagram

Dazu nan aka samu labari Hanan Muhammadu Buhari ta wallafa hoton mahaifinta a Instagram, ta na yabawa mulkinsa da zai zo karshe a mako mai zuwa.

‘Yar shugaban kasar ta na ganin cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya cin ma nasarori a boye a daidai lokacin da wasu masu suka su ke ta caccakarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel