Ana Binciken ‘Dan Takaran Gwamnan da Ya Kashe N2bn Ya Saye Kuri’u a Zaben 2023

Ana Binciken ‘Dan Takaran Gwamnan da Ya Kashe N2bn Ya Saye Kuri’u a Zaben 2023

  • Jam’iyyar APC ta rubutawa ‘Yan sanda korafi cewa Ladi Adebutu ya saye kuri’u a zaben jihar Ogun
  • Jami’an tsaro sun binciki lamarin, kuma sun fara gano kanshin gaskiya a kan ‘dan takaran na PDP
  • Bayanai sun nuna Adebutu ya ware N2bn da aka rabawa mutane ta katin ATM saboda ya ci zabe

Abuja - Yanzu haka jami’an ‘yan sandan Najeriya su na zargin Ladi Adebutu da laifin fitar da makudan kudi da aka yi amfani da su domin sayen kuri’u.

Wani rahoto da Premium Times ta kebanta da shi ya nuna Ladi Adebutu ya ware abin da ya kai Naira biliyan biyu saboda masu zabe su ba shi kuri’unsu..

Adebutu ya tsaya takarar Gwamnan jihar Ogun a zaben da ya gabata, amma bai yi nasara ba, ya zargi jam’iyyar APC da amfani da kudi wajen magudi.

Kara karanta wannan

Fusatattun ‘Yan Takaran Majalisa 7 Sun Fadi Yadda Za Su Karya Bola Tinubu da APC

Zaben 2023
Adebutu, Atiku da Iyochia Ayu wajen kamfe a 2023 Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Wannan zargi ya na cikin korafin da shugaban APC na reshen Ogun, Abdullahi Sanusi ya aikawa Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya a watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Sanusi ya ce ‘dan takaran da PDP ta tsaida ya rika raba katin ATM dauke da N10, 000 da nufin samun karbuwa a wajen masu kada kuri’a a zabe.

Inda aka samu matsala

Zargin da ya fito daga jam’iyyar APC ya na neman jawowa ‘dan siyasar aiki domin ‘yan sanda a karkashin jagorancin Mohammed Babakura sun yi bincike.

DCP Babakura babban jami’in ‘yan sanda ne da yake rike da sashen CID a jihar Ogun.

A sakamakon korafin da aka shigar ne ‘yan sanda da dakarun NDLEA su ka cafke mutane biyar da ake zargin an same su dauke da wannan kati a ranar zabe.

An kama mutane da katin banki

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi: Babu Wanda Zai Iya Hana Rantsar Da Tinubu

An samu wata mai shekara 50, Adejoke Sanni dauke da katin ATM fiye 131, wannan mata da aka samu a yankin Ifo ta na yawo ne da sunan wakiliyar jam’iyya.

Haka zalika rahoton ya ce an cafke Hammed Ogunbona, Waliu Tiamiyu, Owolabi Egunsola da Malik Badmus wadanda ‘yan PDP ne da katin ATM fiye da 50.

Kamar yadda wata ma'aikaciyar bankin da ake bincike, Celestina Appeal tayi wa jami’an tsaro bayani, Adebutu ya na ajiye kudinsa tare da su tun a 2009.

Adebutu ya yi amfani da gyatuma

A cewar Celestina Appeal, a farkon shekarar nan ‘dan takaran ya bukaci bankin ta ba shi kati da sunan zai rabawa mutane kudi domin tunawa da tsohuwarsa.

Adebutu ya fake da Marigayiya Dame Caroline Oladunni Adebutu, ya bukaci katin da aka fi sani da ATM har 200, 000, kuma bankin ya sama masa kafin zabe.

Zaben majalisar wakilai

Kara karanta wannan

‘Yan PDP, LP da NNPP Fiye da 100 Su Na Goyon Bayan ‘Dan Takaran APC a Majalisa

Hon. Yusuf Adamu Gagdi da Hon. Sada Soli sun bayyana matsayar da ‘Yan G7 suka dauka a majalisa, rahoton da mu ka fitar a safiyar Litinin ya bayyana haka.

Masu neman zama shugaban majalisa za su tsaida mutum guda. Ahmed Idris Wase; Muktar Aliyu Betara da Aminu Sani Jaji duka sun tafi a kan wannan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel