Yadda Aka Yi Amfani da Na’urar BVAS, Aka Yaudare Ni a Zaben 2023 – Gwamnan PDP

Yadda Aka Yi Amfani da Na’urar BVAS, Aka Yaudare Ni a Zaben 2023 – Gwamnan PDP

  • Dr. Okezie Ikpeazu yana ganin an yaudare shi da sunan za ayi amfani da fasahar zamani ta BVAS
  • Gwamnan na jihar Abia ya yi takara a PDP, ya sha kashi a takarar Sanata da ya yi a zaben 2023
  • Duk da jam’iyyarsa ta PDP ba tayi nasara ba, Ikpeazu ya bada shawarar a hakura da zuwa kotu

Abia - A wata zantawa da aka yi Dr. Okezie Ikpeazu, Gwamnan ya yi magana a kan takarar Sanata da ya yi da kuma daukacin zaben wannan shekarar.

Mai girma Gwamnan na jihar Abia ya sha kashi a zaben Majalisar dattawa, amma ya shaidawa Daily Trust cewa a hakika, ba shi ne wanda ya yi rashi ba.

Gwamna Okezie Ikpeazu ya dauki siyasa a matsayin hidimtawa al’umma, saboda haka rashin zamansa Sanata zai bude masa kofofin wasu ayyukan.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Tsarge Gaskiya, Ya Fadawa PDP Wanda Ya Jawo Aka Sha Kasa a Zaben 2023

Game da abin da ya faru a takarar da ya yi na Abia ta Arewa, Gwamnan ya zargi na’urar BVAS, yake cewa ba haka ya kamata makomar ta kasance ba.

Gwamnan ya ce a wasu lokutan INEC ta kan dogara da sakamakon cikin BVAS, a wasu lokutankuma sai ayi watsi da su, ya ce aka haka ayi magudi.

A cewarsa, awasu zabukan, babbar jami'ar INEC ta ce zaben bai kammalu ba, daga baya kuma sai ta dawo ta ce an bada umarni ta ayyana sakamakon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan PDP
Peter Obi da Okezie Victor Ikpeazu Hoto: journalist101.com
Asali: UGC

"An yaudare ni da BVAS"

In fada maku gaskiya, ina cikin mutanen da BVAS ta yaudara. Ina cikin wadanda suka yarda da labaran da ake fada a game da na’urar BAS.
Zaben sun sha bam-bam, abin ya yi wahala wannan karo. Bari in ba ku misali, a rumfuna 102 masu rajistar mutane 100, 000, ba a iya yin zabe ba.

Kara karanta wannan

Duk Da NNPP Ta Yi Nasara A Kano Kwankwaso Ya Zargi Buhari Kan Rashin Shirya Zaben Gaskiya

Tazarar da ke tsakanin ‘yan takara ukun farko ba ta kai 30, 000 ba. Idan har ratar ba ta kai-ta kawo ba, to akwai bukatar ayi abin da ya fi dacewa.

- Okezie Ikpeazu

A bar maganar zuwa kotu

A tattaunawar da aka yi da shi, Gwamnan mai barin gado ya nuna ya rungumi kaddara, ya roki wadanda suka sha kasa da su hakura da zuwa kotu.

Sai dai Okezie Ikpeazu ya fadawa jaridar cewa ba a dauki shawararsa ba, har ‘yan takarar LP su na kai PDP zuwa kotun zabe, a ra’ayinsa barnar dukiya ce.

Abba, ni ne Gwamna - Ganduje

A baya an ji labari Gwamnatin Kano ta yi kira ga Abba Kabir Yusuf bayan wata shawara da ya fito ya bada cewa masu gini a filayen gwamnati su daina.

Abdullahi Ganduje ya bukaci zababben gwamnan jihar Kano ya daina yi masa shisshigi, ya ce ya kauracewa yin sanarwar hukuma da sunan bada shawara.

Kara karanta wannan

Bayan Korar Shugaban PDP, Wike Ya Fallasa Facakar Biliyoyin da Aka Yi a 'Yan Watanni

Asali: Legit.ng

Online view pixel