Gwamna Ya Tsarge Gaskiya, Ya Fadawa PDP Wanda Ya Jawo Aka Sha Kasa a Zaben 2023

Gwamna Ya Tsarge Gaskiya, Ya Fadawa PDP Wanda Ya Jawo Aka Sha Kasa a Zaben 2023

  • Gwmanan jihar Abia ya ce babu wanda ya jawo Jam’iyyar PDP ta ji kunya a 2023 illa Peter Obi
  • Okezie Ikpeazu ya ce tun farko ya hango cewa Peter Obi zai kawowa PDP cikas a zaben bana
  • A karshe kuwa haka aka yi, LP ta karbe mulkin Abia daga hannun PDP bayan tsawon shekaru

Abia - Gwmanan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya ce jam’iyyarsa ta PDP mai adawa ta rasa mulkin jihar Abia ne saboda tasirin Peter Obi a siyasar yau.

A wata hira da aka yi da shi a ranar Alhamis a tashar Channels TV, Mai girma Okezie Ikpeazu ya shaida cewa guguwar Peter Obi ce ta yi waje da PDP.

Dr Alex Otti ya lashe zaben sabon Gwamnan Abia, zai karbi mulki a hannun Okezie Ikpeazu wanda ya so a ce jam’iyyarsa ta zarce a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Akwai Aiki a Gaban NNPP a Kano, APC Za Ta Karbe Nasarar Abba a Zaben Gwamnan 2023

Guguwar Peter Obi ce. Nayi hasashen hakan, kuma na fadawa jam’iyya ta. Na fito na fada cewa babu ‘dan siyasar da zai yi wasa da abin da Peter Obi yake yi.
Makomar LP ta na hannun Peter Obi a yau, ya danganta da yadda ya kula da talakawan da ya samu goyon bayansu da yadda zai yi amfani da su ga burinsa.

Rikicin G5 a PDP

A tattaunawar da aka yi da shi, Ikpeazu ya ce bai taba nadamar shiga kungiyar Gwamnonin PDP na G5 da ta ki goyon bayan takarar Atiku Abubakar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Abia
Gwamna Okezie Ikpeazu
Asali: UGC

Gwamnan da ya sha kashi a zaben Sanata ya ce bai taba bata ‘dan takaran shugaban kasar na LP a wajen kamfe ba, domin yana so mulki ya bar Arewa.

A zaben Sanata, Enyinnaya Abaribe na jam’iyyar APGA ya hana Ikpeazu tafiyar majalisar dattawa, ya ce tun da mulki ya koma Kudu, bai da asara.

Kara karanta wannan

Bayan Korar Shugaban PDP, Wike Ya Fallasa Facakar Biliyoyin da Aka Yi a 'Yan Watanni

Daily Trust ta rahoto Gwamna Ikpeazu yana mai cewa yakar ‘dan takaran da jam’iyyarsa ta tsaida yana cikin mafi kyawun matsayar da ya dauka.

Alex Otti yana da ja

Amma da aka zanta da shi, Dr Alex Otti ya nuna ko babu Obi zai ci zaben Gwamna domin saura kiris ya kai labari a karkashin jam’iyyar APGA a 2015.

Dr. Otti ya ce ko a lokacin da ya shiga jam’iyyar adawa ta LP, Obi bai bar PDP ba tukuna.

APC za ta kotu a Kano

An ba Abba Kabir Yusuf da Aminu Abdulsalam Gwarzo satifiket din lashe zaben Gwamna, amma rahoto ya zo cewa APC ta rantse sai ta zarce a Kano.

Ahmad Aruwa wanda shi ne Kakakin APC na Kano, ya ce za su kalubalanci sakamakon zaben Shugaban kasa da na Gwamna da NNPP tayi nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel