Duk Da NNPP Ta Yi Nasara A Kano Kwankwaso Ya Zargi Buhari Kan Rashin Shirya Zaben Gaskiya

Duk Da NNPP Ta Yi Nasara A Kano Kwankwaso Ya Zargi Buhari Kan Rashin Shirya Zaben Gaskiya

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a zaben Fabrairun 2023 ya zargi Shugaba Buhari kan rashin shirya sahihin zabe
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi wannan zargin ne yayin jawabinsa da ya yi wurin taron bayan zabe na farko da jam'iyyar ta NNPP ta yi a birnin tarayya Abuja
  • Jagoran na jam'iyyar NNPP na kasa, amma, ya ce yana fatan kotu za ta share wa talaka hawaye sannan ya yi kira ga shugabanni a jam'iyyarsa su fara aiki gabanin zabe na gaba a shekarar 2027

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a zaben shugaban kasa da yan majalisu da aka yi a ranar Asabar 5 ga watan Fabrairu, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Shugaba Muhammadu Buhari, yana cewa shugaban kasar bai yi abin da kamata ba don samar da sahihin zabe na adalci, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan Korar Shugaban PDP, Wike Ya Fallasa Facakar Biliyoyin da Aka Yi a 'Yan Watanni

Kwankwaso ya ce a kasashen da suka cigaba, da irin siyan kuri'a da tsorata masu zabe da bindiga da matsaloli da aka samu, da an soke zaben, a yayin da ya ce sakamakon zaben shugaban kasar bai yi daidai da abin da yan Najeriya ke so ba.

Rabiu Kwankwaso
Kwankwaso Ya Zargi Buhari Kan Rashin Shirya Zaben Gaskiya A 2023. Hoto: Daily Trust
Asali: Getty Images

Amma, ya roki bangaren shari'a ta cigaba da kasancewa wuri na karshe da talaka zai tafi ya samu sa'ida, kada a maimaita yadda wanda ya zo na hudu a zabe ya yi nasara a cewar kotun koli, yana nuna fargabar yanzu ma dole ne a yi adalci ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis a Abuja a taron farko na bayan zabe na Kwamitin Shugabannin Jam'iyya, NEC.

Tsohon gwamnan na jihar Kano kuma Sanata ya zargi jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da yin magudi a sakamakon zabe a wasu jihohi, musamman zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaɓen Gwamnoni Na 2023: Jerin Zaɓaɓbun Gwamnoni 5 Da Suka Ci Zaɓe Da Ƙuri'u Mafi Ƙaranci

Ya ce zaben bai yi daidai da 'abin da yan Najeriya da dama ke so ba.'

Kwankwaso, wanda shine jagoran jam'iyyar na kasa, ya yi kira ga shugabannin NNPP su yi amfani da damar da suke da shi su fara shirin zabe mai zuwa a 2027 ta hanyar zage damtse, su koma yankunansu su kara yin aiki.

Ba zan saka baki a mullkin Abba Gida-Gida ba - Kwankwaso

Sanata Rabiu Kwankwaso, jagoran jam'iyyar NNPP na kasa ya ce ba zai tsoma baki a harkokin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, zababben gwamnan jihar Kano ba duk da kasancewarsa uban gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel