Abba Gida-Gida Ya Yi Nadin Mukamin Farko Bayan Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano

Abba Gida-Gida Ya Yi Nadin Mukamin Farko Bayan Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano

  • Abba Kabir Yusuf ya zabi Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya ba shi mukamin babban Sakatare
  • Bature Dawakin-Tofa zai zama Sakataren yada labarai na lokacin da ake shirin karbar mulkin Kano
  • Zababben Gwamnan na Kano ya ce sabon sakataren ya dace da wannan kujera, duba da tarihinsa

Kano - A ranar Alhamis, Abba Kabir Yusuf ya bada sanarwar nada Sunusi Bature Dawakin-Tofa a matsayin Babban sakatare na lokacin karbar mulki.

Vanguard ta ce sanarwar nadin mukamin ta fito da shugaban kwamitin karbar mulkin jihar Kano a madadin zababben Gwamna, Abba Gida Gida.

Kwamitin ya bayyana wannan nadin mukami a matsayin wanda ya dace, la’akari da cancanta, kokari da irin rikon amanar Sunusi Bature Dawakin-Tofa.

Kafin yanzu, sabon Sakataren kwararren ‘dan jarida ne wanda ya yi shekaru 19 a wannan aiki, ya samu kwarewa a kamfanonin gida da wajen Najeriya.

Kwararren 'dan jarida ne

A shekarar 2008, Dawakin-Tofa ya lashe kyautar da Cambridge ta shirya na ‘yan jarida masu binciken kwa-kwaf, bayan nan ya yi aiki da kamfanoni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga cikin wuraren da Hadimin ya yi aiki akwai ofishin cigaban hulda da jakadancin Birtaniya na FCDO, kungiyar USAID da gidauniyar Melinda Gates.

Abba Gida-Gida
Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa, A. A Gwarzo Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook

Bugu da kari, Dawakin-Tofa ya taba yin aiki da kungiyoyin ketare na Save the Children Int'l, Discovery Learning Alliance da gidauniyar Rockefeller.

Rahoto ya ce ‘dan jaridar ya rike mukamin Babban Manaja a kamfanin Dantata Foods & Allied Products Limited (DFAP) da kuma Darekta a YieldWise Project.

Daya daga cikin hadimin Rabiu Musa Kwankwaso, Mal. Ibrahim Adam ya tabbatar da wannan nadin mukami a yammacin yau a shafinsa na Facebook.

Dawakin Tofa ya yi aikace-aikace da suka shafi yyada labarai, hulda da jama’a da sauransu. Yanzu shi ne mataimakin shugaban Kingston Organic PLC.

Tarihin karatun boko

A bangaren ilmi, Dawakin Tofa ya yi digiri a ilmin aikin jarida a jami’ar Maiduguri, kafin nan yana da diflomomi daga makarantar Kaduna Polytechnic.

Baya ga haka, ya samu digirin digirgir a harkar cigaban al’umma daga LAUTECH da digirgir a kan hulda da jama’a daga BUK, sannan ya yi karatu a waje.

Rikicin shugabanci a PDP

Rahoto ya zo a baya cewa akwai yiwuwar Iyorchia Ayu ya koma kan kujerarsa, domin kuwa shugaban PDP na kasa, bai yi murabus daga matsayinsa ba.

Hadimin Shugaban jam’iyyar ta PDP, Simon Imobo-tswam ya ce Mai gidansa zai je kotu ayi shari’a. Sanata Dino Melaye ya tabbatar da haka da yake martani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel