Iyorchia Ayu Ba Zai Sallama Cikin Sauki ba, Hadiminsa Ya Fadi Shirin Shugaban PDP

Iyorchia Ayu Ba Zai Sallama Cikin Sauki ba, Hadiminsa Ya Fadi Shirin Shugaban PDP

  • Dr. Iyorchia Ayu yana iya dawowa kan kujerarsa da ya bari ta Shugaban jam’iyyar PDP na kasa
  • Simon Imobo-tswam ya nuna uban gidansa, Ayu zai kare kan shi a shari’ar da ake yi a kotun Jiha
  • Dino Melaye ya ce masu murna su dakata domin shugaban na PDP bai yi murabus ba tukuna

Benue - Shugaban jam’iyyar PDP na kasa wanda ya sauka daga kujerarsa, Iyorchia Ayu ya shirya kalubalantar dakatar da shi da aka yi a gaban kotu.

Punch ta kawo rahoto cewa Dr. Iyorchia Ayu zai kare kan shi a babban kotun jihar Benuwai mai zama a Makurdi wanda ta zartar da hukunci a kan sa.

A ranar Litinin, wani Hadimin shugaban jam’iyyar hamayyar, Simon Imobo-tswam ya shaidawa manema labarai cewa mai gidan na sa zai tafi kotu.

Kara karanta wannan

Toh fa: Sanata ya ba da shawarin a ba Buhari wata babbar kujera a Najeriya bayan mika mulki

Simon Imobo-tswam shi ne mai ba Iyorchia Ayu taimako na musamman a harkokin sadarwa.

Ba za a tsaya a haka ba

Jim kadan bayan an nada Umar Damagum a matsayin wanda zai zama shugaban rikon kwarya, mai bada shawarar ya fadi matakin da za su dauka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Domin ganin ya dawo kan kujerarsa, Imobo-tswam ya nuna Ayu zai dauki hayar Lauyoyi domin su kare shi a shari’ar da ake yi a babban kotun jihar.

Iyorchia Ayu
Atiku, Ayu da Okowa a taron PDP Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Alkali ya haramtawa Dr. Ayu shiga ofis a matsayin shugaban jam’iyya na kasa a dalilin dakatar da shi da shugabannin PDP na mazabar Igyov suka yi.

Hakan na zuwa ne bayan tsohon Mai ba Gwamnan Benuwai shawara, Conrad Utaan, ya shigar da kara domin kawo karshen wa’adin shugaban na PDP.

Iyorchia Ayu da jam’iyyar PDP ne wadanda za su kare kan su a karar. Jaridar ta ce sai ranar 17 ga watan Afrilun 2023 sannan kotun za ta sake yin zama.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka Daga Kujararsa, An Maye Gurbinsa Nan Take

Kafin nan, an ji Dino Melaye yana cewa yadda shugaban na PDP da aka dakatar ya sauka daga kan kujerarsa ya nuna jam’iyyarsu ta yadda da bin doka.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugabancin kasar a zaben 2023, ya ankarar da ‘yan taware cewa Ayu bai yi murabus, ya bada wuri ne kurum.

Tinubu ya cika 71 a yau

A rahoton da muka fitar, an ji cewa a yau babu bidiri ko sharholiyar da za ayi yayin da ranar haihuwar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ta zagayo.

Wata sanarwa ta nuna za ayi amfani da yau wajen yin addu’o’i da karatun kur’ani da hudubobi. Malamai za su yi addu’o’i domin samun cigaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel