Inyamuri Ya Samu Nasara a Zaben Jihohi, Ya Ci Kujerar Majalisa a Arewacin Najeriya

Inyamuri Ya Samu Nasara a Zaben Jihohi, Ya Ci Kujerar Majalisa a Arewacin Najeriya

  • Nelson Len wanda asalin Ibo ne, zai wakilci mutanen Nguroje a majalisar dokokin jihar Taraba
  • Len ya yi galaba a kan ‘dan majalisa mai-ci na jam’iyyar PDP, ya zama zababben ‘dan majalisa
  • Jam’iyyun SDP da kuma NNPP sun samu kujeru a majalisar dokokin a zaben 2023 da aka gudanar

Taraba - Akwai wani mutumin Ibo mai suna Nelson Len da ya yi nasara a zaben ‘yan majalisar dokoki da aka shirya a jihar Taraba.

A ranar Laraba, 22 ga watan Maris 2023, Daily Trust ta kawo labari cewa Nelson Len ya zama zababben ‘dan majalisar dokokin jiha.

Len wanda asalinsa mutumin Kudu maso gabashin Najeriya ne ya lashe kujerar ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Nguroje a Taraba.

Abin ban mamakin shi ne ‘dan siyasar ya yi nasara ne a kan Barista Bappe Muhammed wanda shi ne ‘dan majalisa mai-ci.

Kara karanta wannan

Sa’o’i Kadan da Kammala Zabe, Sanata Ya Fice Daga PDP, Ya Rungumi Tinubu da Kyau

Honarabul Bappe Muhammed ya sha kashi ne a hannun jam’iyyar PDP. Legit.ng Hausa ta fahimci Mista Len hadimin Gwamna ne.

Mata 2 sun ci kujeru a Taraba

Rahoton ya kuma tabbatar da an samu wasu mata biyu Hajiya Batulu Muhammed da Borinica Alhassan da suka yi nasara a zaben bana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Batulu Muhammed za ta wakilci mazabar Gashaka a karkashin jam’iyyar APC yayin da Alhassan ta lashe kujerar Bali a inuwar PDP.

Siyasa
Taron siyasa a Najeriya Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

PDP ta na da rinjaye

A karshen zaben ‘yan majalisar da aka shirya na ranar Asabar, jam’iyyar PDP ta cigaba da rike rinjaye a majalisar Taraba da ‘ya ‘ya 14.

Jam’iyyar APC ta samu ‘yan majalisa bakwai sai kuma NNPP mai alamar kayan dai ta na da biyu, sai jam’iyyar SDP ta samu kujera guda.

Kara karanta wannan

Matasan ‘Yan Majalisa: ‘Yan shekara 26 Zuwa 30 Sun Kunyata Dattawa a Kwara, Yobe, Ogun

Babu mamaki NNPP ta iya samun nasara ne a dalilin tsaida Sani Yahaya da tayi a takarar Gwamna wanda ya zo na biyu da kuri’u 202,277.

Ita ma SDP mai kujera daya a majalisar dokokin ta tsaida Danladi Baido Tijo a zaben Gwamna.

Amurka tana so a dauki mataki

Binciken da Amurka tayi ya nuna an samu tashin-tashina a wasu Jihohi. Rahoto ya zo cewa ana so hukunta duk masu hannu wajen murdiya.

Baya ga haka, jakadancin kasar wajen yana zargin Kabilanci ya yi aiki a zaben Gwamna da aka yi a jihar Legas, inda jam’iyyar APC ta ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel