Sa’o’i Kadan da Kammala Zabe, Sanata Ya Fice Daga PDP, Ya Rungumi Tinubu da Kyau

Sa’o’i Kadan da Kammala Zabe, Sanata Ya Fice Daga PDP, Ya Rungumi Tinubu da Kyau

  • Chimaroke Nnamani ya katse alakarsa da Jam’iyyar PDP bayan an doke shi a zaben Majalisa
  • Kafin a kai ga haka, Sanatan ya jawo fushin PDP da ya fito fili yana marawa Bola Tinuub baya
  • Sanata Nnamani ya fitar da jawabi cewa yana tare da zababben shugaban kasa na Jam’iyyar APC

Abuja - Bayan watanni hudu ana haka-haka da shi a PDP, tsohon Gwamna Chimaroke Nnamani ya zabi ya fice daga jam’iyyar adawa.

Sanata Chimaroke Nnamani ya fitar da jawabi da hannunsa wanda ya shiga hannun jaridar Vanguard a safiyar ranar Litinin dinnan a Abuja.

Chimaroke Nnamani wanda ya fito karara yana goyon bayan Asiwaju Ahmed Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023, ya fusata jam’iyyar PDP.

Takardar da ta shiga hannun manema labarai dazu ta nuna ‘dan siyasar ya bar PDP ne kusan sa’o’i 24 bayan shan kashi a zaben majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Ganduje Ya Fadawa Kanawa Su Zabi Abba Gida-Gida a Gobe

‘Dan takaran LP ya doke tsohon Gwamnan na Enugu a kujerar Enugu ta yamma a zaben 2023.

Nnamani ya yi amfani da jawabin wajen godewa mutanen mazabarsa a jihar Enugu da suka rika ba shi goyon bayansu na tsawon shekaru a siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chimaroke Nnamani
Chimaroke Nnamani da Bola Tinubu Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Mutanensa za su bar PDP

Sanata Nnamani yake cewa ya tuntubi al’ummar mazabarsa da abokan siyasa, kuma duk sun gamsu su sauya-sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP.

Kamar yadda rahoto ya zo, dalilin sauya-shekar kuwa shi ne ‘dan majalisar dattawan ya ce su na da sabani shugabannin jam'iyyar PDP na kasa.

‘Dan majalisar ya yi godiya ta musamman ga gidan siyasarsa na Ebeano da suke tare da shi tun fil azal.

Nnamani ya bi Tinubu

Tsohon Gwamnan ya tabbatar da hadewarsa da zababben shugaban kasa, Asiwaju Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin zai cigaba da hada-kai da shi.

Kara karanta wannan

'Dan takaran Sanatan APC a Kaduna Zai Tafi Kotu, Ya Fito da Hujjojin Magudin PDP

Sanata Nnamani ya nuna sa ran shi na gwamnatin Tinubu zai kawo mulkin cigaba, bin doka da kuma kare hakkin Bil Adama domin ‘Yan Najeriya.

Zaben Gwamna a Adamawa

Festus Keyamo ya ce an hada-baki da ‘yan sanda da DSS domin a hana Aisha Dahiru Binani samun nasara a zaben Gwamnan jihar Adamawa na 2023.

A cewarsa, Kwamishinan ‘yan sanda da Darektan Hukumar DSS sun je ofishin INEC REC domin Gwamna ya huro wuta a zaftarewa APC kuri’u a Fufore.

Asali: Legit.ng

Online view pixel