Matasan ‘Yan Majalisa: ‘Yan shekara 26 Zuwa 30 Sun Kunyata Dattawa a Kwara, Yobe, Ogun

Matasan ‘Yan Majalisa: ‘Yan shekara 26 Zuwa 30 Sun Kunyata Dattawa a Kwara, Yobe, Ogun

  • Rasheed Buruji Kashamu wanda matashi ne ya samu kujerar majalisar dokoki a PDP a jihar Ogun
  • Misis Rukayat Motunrayo Shittu za ta wakilci mazabar Owode da Onire a majalisar jihar Kwara
  • Shugaban majalisar Yobe, Rt. Hon. Ahmad Lawal Mirwa ya rasa kujerarsa ga ‘Dan shekara 34 a Nguru

Abuja - Zaben bana ya zo da abubuwan ban mamaki musamman tun da aka kawo dokar da ta rage shekarun masu tsayawa takarar siyasa a Najeriya.

A jihar Ogun, Rasheed Buruji Kashamu aka tsaida a matsayin zababben ‘dan majalisar Ijebu ta Arewa I, Daily Trust ta kawo wannan rahoto dazu.

Rasheed Buruji Kashamu wanda yana cikin ‘ya ‘yan Marigayi Buruji Kashamu zai zama ‘dan auta a majalisar dokokin jihar Ogun a farkon Yunin 2023.

Haka zalika rahoto ya zo cewa Yusuf Amosun ya lashe zaben ‘dan majalisar Ewekoro a jihar Ogun, shi kuma ya yi nasara ne a jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Shiga Neman Tsohon Gwamna Kan ‘Kisan Kai da Garkuwa da Mutane’

Rukayat Motunrayo Shittu
Rukayat Motunrayo Shittu ta zama ‘Yar Majalisa @Rukayatshittu06
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yusuf Amosun yaro ne ga tsohon Gwamnan jihar kuma Sanata mai-ci, Ibikunle Amosun.

Budurwa ta samu kujera a Kwara

Idan aka koma jihar Kwara, za a ji yadda Rukayat Motunrayo Shittu ‘yar shekara 26 tayi nasara a zaben majalisa na mazabar Owode/Onire a yankin Asa.

Rukayat Motunrayo Shittu wanda aka haifa a 1996 ta doke Abdullah Magaji da PDP ta tsaida.

Wannan Baiwar Allah tayi Difloma a ilmn yada labarai da addinin musulunci a 2015, a shekarar 2017 ta shiga jami’ar NOUN, ta kammala a 2022.

The Cable ta ce kafin zababbar ‘yar majalisar ta samu wannan nasara, sai da aka yi ta kai ruwa rana, domin ta je kotu a kan samun tikitin APC.

Majakura zai wakilci Nguru waje

Legit.ng Hausa ta samu labari wani mai shekara 34 a Duniya ne ya doke Rt. Hon. Ahmad Lawal Mirwa a zaben majalisar dokoki na Nguru II a Yobe.

Kara karanta wannan

Doguwa, Wase da ‘Yan Majalisa 5 a Arewa Sun Kwallafa Rai Kan Kujerar Gbajabiamila

‘Dan takaran APC a zaben, Rt. Hon. Ahmad Lawal Mirwa shi ne shugaban majalisar jiha, kuma tun 2003 yake majalisa, ya rasa takararsa ta shida.

Daily Trust tace Lawan Musa wanda ya yi fice wajen sukar Mirwa ya yi takarar Kansila a Majakura a APC, da bai yi nasara ba, sai ya shiga PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel