Tsohon Mataimakin Ganduje Ya Fadawa Kanawa Su Zabi Abba Gida-Gida a Gobe

Tsohon Mataimakin Ganduje Ya Fadawa Kanawa Su Zabi Abba Gida-Gida a Gobe

  • Farfesa Hafiz Abubakar ya yi kira ga Kanawa su fita gaba dayansu domin su kada kuri’a a gobe
  • Tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kano ya nuna Jam’iyyar NNPP yake goyon baya a 2023
  • Abubakar ya fadawa al’umma su Abba Kabir Yusuf, su kuma kare kuri’unsu a zaben da za ayi

Kano - Farfesa Hafiz Abubakar ya yi wa takarar Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigeria People’s Party watau NNPP a jihar Kano mubaya’a.

A rahoton Daily Nigerian na daren Asabar, an ji labari Farfesa Hafiz Abubakar yana goyon bayan Abba Kabir Yusuf ya zama Gwamna a jihar Kano.

Hafiz Abubakar ya bayyana goyon bayansa ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan rediyon Express Radio FM da ke Kano a yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

Allura Na Kokarin Tona Garma a Zargin Cinye N500m Na Kamfe a Jam’iyyar APC

Tsohon mataimakin Gwamnan na jihar Kano ya ce gwamnatin da ke mulki a Kano a karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasa ta ba al’umma kunya.

An wahala a mulkin APC

An rahoto Farfesan yana mai zargin cewa gwamnati mai-ci ta jefa mutane cikin wahala na babu gaira babu dalili a tsawon shekaru takwas da tayi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kiran da Hafizu Abubakar ya yi wa Kanawa a ranar ja-ji-birin zaben sabon Gwamna shi ne kowa ya fita ya kada kuri’arsa, kuma su fatattaki APC a Kano.

Abba Gida Gida
Abba Kabiru Yusuf Hoto: KingsPhotography
Asali: Facebook

‘Dan siyasar ya bukaci mutane su canza Gwamnati game da yin hakan ba tare da tada rigima ba, kuma ka da su bari wasu su yi masu magudin zabe.

'Yan APC za su iya magudi

"Ina kira ga mutanen jihar Kano su fito kwansu da kwarkatarsu su zabi jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Tsorata Kafin Ranar Zabe, Ya Kai Karar ‘Dan Takaran APC Wajen Buhari

Kuma ka da su bari wani ya murde zaben domin mutanen nan (‘yan jam’iyyar APC) za su iya komai domin su yi magudi a zaben nan.

Tsakanin 2015 da 2018, Farfesa Hafiz Abubakar shi ne mataimakin Gwamnan Kano. Daga baya sai Abdullahi Ganduje ya canza shi da Nasiru Gawuna.

Siyasar Kaduna a 2023

Rahoto ya zo cewa Muhammad Sani Abdullahi da ya yi takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya a jam'iyyar APC zai shigar da karar PDP da INEC a kotu.

Muhammad Sani Abdullahi ya ce sun lura an saba doka, an yi magudi da rashin bin tsarin dokar zabe da kuma kin amfani da na’urar zabe a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel