Binani: Minista Ya Yi Maganar Makarkashiyar da PDP ke Shiryawa a Zaben Adamawa

Binani: Minista Ya Yi Maganar Makarkashiyar da PDP ke Shiryawa a Zaben Adamawa

  • Karamin Ministan samar da ayyukan yi ya zargi Gwamnatin Adamawa da shirya magudin zabe
  • Festus Keyamo ya ce ana kokarin amfani da ‘yan sanda da DSS domin PDP ta zarce a Adamawa
  • Ministan ya yi magana a Twitter, yake cewa ana so INEC ta hana Aisha Dahiru Binani kai labari

Delta - Festus Keyamo wanda Minista ne a gwamnatin tarayya, kuma jigo a tafiyar APC, ya tsoma baki a kan batun siyasar jihar Adamawa.

Festus Keyamo esq wanda ya kada kuri’arsa a zaben Gwamnan jihar Delta ya fito yana maganganu cikin tsakar daren Litinin a shafin Twitter.

Ministan ya ce ba za a yarda da abin da ake kokarin yi wa Aisha Dahiru Binani a zaben gwamna ba.

Bayan ya fadi haka kuma, an ji kakakin kwamitin yakin zaben shugaban kasar na APC yana cewa an hada baki da jami’an tsaro ayi murdiya.

Kara karanta wannan

2023: Yadda Ta Kaya da Manyan Masu Neman Takara a Akwatinsu a Zaben Jihohi

Kwararren Lauyan yake cewa an hada-kai da Kwamishinan ‘yan sanda da Darektan DSS saboda a rage yawan kuri’un jam’iyyar APC a Fufore.

Ba ZA A YARDA da abin da yake faruwa a Adamawa ga Sanata Aisha Dahiru Binani ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahotanni na zuwa cewa Gwamna Ahmadu Fintiri ya matsawa jami’an INEC lamba da su canza sakamakon karamar hukumar Fufore domin a rage tazarar da ta bada a takarar Gwamna.
Binani
Binani ta na kamfe Adamawa Hoto: thisdaylive.com
Asali: Twitter
Macen farko da ta taba kawo wannan mataki a zabe! DOLE INEC TA FASA WANNAN AIKI!
Rahotanni na zuwa cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa da Darektan DSS su na ofishin INEC REC wajen tattara sakamako, Gwamna Fintiri ya huro masu wuta su taba sakamakon zaben karamar hukumar Fufore inda aka zaftarewa Sanata Binani kuri’u 11, 000.

- Festus Keyamo

Sanatan Adamawa ta tsakiya, Aisha Binani ta na neman Gwamnan Adamawa a karkashin APC mai mulkin kasa, ta na takara da Gwamna mai-ci.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Harin Wurin Raba Kayayyakin Zabe, Sun Tafka Barna

Zaben jihar Nasarawa

Abdullahi A. Sule ya yi nasara a zaben Gwamnan Jihar Nasarawa da aka shirya a makon jiya, Gwamnan zai cigaba da mulki zuwa Mayun 2023.

Rahoton ya tabbatar da cewa burin David Ombugadu na zama Gwamna bai tabbata ba, jam’iyyar PDP ta nuna za ta shigar da kara a kotun karar zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel