Mukarrabin Jonathan Ya Fadi Yaudarar da Tinubu ya yi Amfani da Ita Wajen Doke Atiku

Mukarrabin Jonathan Ya Fadi Yaudarar da Tinubu ya yi Amfani da Ita Wajen Doke Atiku

  • Reno Omokri ya ce babu wata hanyar da Peter Obi zai bi ya iya zama Shugaban Najeriya a 2023
  • Tsohon hadimin na Goodluck Jonathan ya ce LP ta taimakawa Bola Tinubu wajen samun nasara
  • A cewar Omokri ‘Dan takaran na APC ne ya yaudari Obi da nufin a rage kuri’un PDP a zaben bana

Abuja - Reno Omokri ya yi aiki da Goodluck Jonathan a matsayin mai bada shawara, ya fito yana bayanin abin da ya faru a zaben da aka yi.

Tribune ta rahoto tsohon hadimin yana cewa jam’iyyar APC tayi amfani da LP wajen lashe zabe.

Fasto Reno Omokri ya shaida cewa Asiwaju Bola Tinubu da ya lashe zaben shugaban kasa ne ya yaudari Peter Obi ya shiga takara a zaben 2023.

Hadimin tsohon shugaban na Najeriya ya ce Bola Tinubu ya yi hakan ne domin ganin ya rage karfin kuri’un da jam’iyyar hammaya za ta samu.

Kara karanta wannan

Na boye ya ya bayyana: Jigon APC ya yi sakin baki, ya fadi dalilin nasarar Bola Tinubu

"LP ba za ta iya karbar mulki ba"

A cewar Omokri, babu ta yadda Obi zai iya yin nasara a zaben shugaban kasar, illa iyaka ya karbe wasu kuri’un da ya kamata PDP ta amfana da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan maganarsa ta tabbata, Tinubu ya yi amfani da wasu abokan kasuwanci ne wajen zuga Obi ya shiga neman kujerar shugabancin kasar.

Obidients
Asiwaju Tinubu da Peter Obi Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Faston yake cewa zababben shugaban na Najeriya ya yi amfani da magoya bayan ‘dan takaran LP wadanda aka fi sani Obidients wajen cin ma burinsa.

Daily Post ta rahoto Omokri yana cewa ‘Yan Obidients ba su iya gane tarkon ‘dan takaran ba.

Jawabin Reno Omokri

"Babu hanyar da Peter Obi zai bi, ya lashe zabe. Bai da karbuwa a fadin Najeriya. Tinubu ya san wannan.
Sai ya yi amfani da abokan kasuwancinsa da ke tare da shi, ya yaudari Peter Obi ya shiga zabe, ya san ta haka ne kurum za a rage kuri’un PDP.

Kara karanta wannan

Sakataren APC Ya Fadi Abin da Ya Taimaki Bola Tinubu, Ya Doke Atiku Abubakar da Obi

Kuma Tinubu ya yi amfani da kwarewarsa wajen wasa da hankalin gama-garin ‘Yan Obidient. Ba su da kan-kan da kan da za su fahimci an yi amfani da su ne.”

- Cewar Reno Omokri

LP ta bata ruwa, ba ta sha ba

A karshe dai dabarar nan tayi tasiri domin Atiku Abubakar da Peter Obi sun tashi da kuri’u miliyan 13, yayin da APC kuwa ta samu miliyan takwas.

Idan za ku iya tunawa, rahoto ya zo cewa 'Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ne ya samu nasara a zaben jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel